Sri Lanka: Masu zanga-zanga sun mamaye fada har sai shugabanni sun sauka

2
304

Dubban mutane ne suka yi zanga-zanga a Colombo a ranar Asabar inda suka buƙaci ya yi murabus bayan shafe watanni ana zanga-zangar.

Sunshiga gurin shakatawa suna iyo

Masu zanga-zangar sun ce za su ci gaba da mamaye gidajen shugaban ƙasa da na firaministan ƙasar Sri Lanka, har sai shugabannin biyu sun yi murabus a hukumance. Shugaba Gotabaya Rajapaksa ya ce zai sauka daga mulki ranar 13 ga watan Yuli, kamar yadda kakakin majalisar ya bayyana a ranar Asabar.

Gasu a ɗakunan gidan shugaban

Ana dai zargin shugaban kasar ne da tabarbarewar tattalin arzikin kasar, wanda ya janyo karancin abinci da man fetur da kuma magunguna tsawon watanni.

Sai dai ba a ga shugaban ko kuma waninsa ya yi wata sanarwa da kansa ba. Wasu majiyoyin soji sun shaida wa BBC cewa a halin yanzu yana cikin wani jirgin ruwan sojin ruwa a ruwan kasar Sri Lanka. Majiyoyin sun ce dan uwansa, tsohon Firayim Minista Mahinda Rajapaksa, yana sansanin sojin ruwa a ƙasar.

Inda suketa kallo cikin nutsuwa

Shi ma Firayim Minista na yanzu Ranil Wickremesinghe ya ce zai sauka daga mukaminsa biyo bayan zanga-zangar da aka yi ranar Asabar, inda aka ƙona gidansa na ƙashin kansa. Sai dai masu zanga-zangar na ci gaba da nuna shakku kan manufar shugabannin.

2 COMMENTS

Leave a Reply