Sojoji sun kuɓutar da ‘yar makarantar Chibok a Borno, bayan shekara takwas da saceta

1
823

Sojojin Najeriya sun sake ceto wata ‘yar makaranta da aka yi garkuwa da su a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati, Chibok, shekaru takwas bayan sace su a shekarar 2014.

Rundunar Sojojin Hadin Kai ta gano Ruth Bitrus. Sun ce Ruth Bitrus ta kuɓuta daga hannun ‘yan Boko Haram da yaronta. Kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar GC Musa ne ya bayyana haka a Barikin Maimalarin a lokacin bikin miƙa kayan aikin jinya da hukumar raya arewa maso gabas ta yi domin tallafa wa sojoji a ranar Laraba.

Ya ce: “Za ku iya tunawa cewa a makonnin da suka gabata mun kubutar da ‘yan matan Chibok biyu da ‘ya’yansu, zan so in sanar da ku cewa mun kubutar da wata a yayin gudanar da ayyukanmu. “Ba za mu huta ba har sai an dawo da Leah Shaibu da sauran ‘yan matan Chibok tare da hada kan iyalansu. Ba za mu huta ba har sai an dawo da su lafiya.

“An ceto Ruth Britus daga dajin Sambisa tare da ɗanta,” inji Manjo Janar Musa. A cikin watan Yuni ne sojojin suka ceto ‘yan matan Chibok biyu Mary Dauda da Hauwa Joseph bayan sun tsere daga sansanin ‘yan Boko Haram da ke Gazuwa mai tazarar kilomita tara daga karamar hukumar Bama ta Borno.

1 COMMENT

Leave a Reply