Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gudanar da taron gaggawa kan barazanar tsaro a birnin Abuja

2
316

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da jami’an tsaro biyo bayan gargaɗin da manyan ƙasashen duniya suka yi na yiwuwar kai hare-haren ta’addanci ƙasar.

A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan kafafen yada labarai Malam Garba shehu ya fitar, ya ce a yayin ganawar shugaban ƙasar zai saurari bayanai daga manyan hafsoshin tsaron, tare da ƙara ƙaimi a fannonin da ke buƙatar kulawa.

A kwanakin da suka gabata ne manyan ƙasashe kamar Amurka, da Birtaniya, da Canada suka gargaɗi ƴan kasarsu da su yi taka-tsantsan saboda sun samu bayanan da ke cewa za a kai hare-hare a ƙasar, musamman ma a Abuja, babban birnin ƙasar.

Ƙasar Amurka a nata ɓangaren ta buƙaci ma’aikatan ofishin jakadancin ƙasar a Najeriya su fice daga Abuja.

2 COMMENTS

Leave a Reply