Dalilin da ya sa na wakilta su El-Rufai su amsa min tambayoyi a Chatham House – Tinubu

1
325

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa ya wakilta wasu ‘ya’yan jam’iyyar su amsa masa tambayoyin da aka yi masa.
A cewar tsohon gwamnan na Legas, ya yi amfani da hanyar tawagarsa don nuna hadin gwiwa.

Tinubu ya yi magana ne a wurin laccar Chatham House mai taken: ‘Zaɓen Najeriya na 2023 a Landan.

A wajen laccar, Tinubu bayan jawabin buɗe taron, ya tura wa gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai tambayar da aka masa kan yadda gwamnatinsa (Tinubu) za ta magance matsalar rashin tsaro, ya kuma turawa daraktan yaɗa labarai na ƙungiyar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Dele Aleke, tambayar da aka masa kan satar manfetir.

Tinubu ya kuma wakilta tsohon kwamishinan kuɗi a jihar Legas, Wale Edun, da ya amsa tambaya kan yadda shi (Tinubu) zai bunƙasa tattalin arzikin ƙasar idan aka zaɓe shi.

Sauran sun haɗa da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila; tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi; Shugabar Mata ta APC ta Ƙasa, Dr Betta Edu; sun kuma amsa masa tambayoyin.

Tinubu ya ce: “Bari in nuna a nan ɗaya daga cikin falsafa da koyaswar da na yi imani da su sosai, shi ne yin haɗin gwiwa, idan an yi haɗin gwiwa a ƙungiyance ba za a iya rarrabuwa ba, don nuna hakan, zan ba da tambayoyin ga ƙungiyar.

“A bangaren ilimi kuwa, Tinubu ya yi alkawarin bayar da rance wa ɗaliɓai tare da gyara tsarin karatun Almajirai da ake yi a arewacin Najeriya.

El-Rufai wanda ya amsa tambayoyi kan harkokin tsaro, ya bayyana cewa, ‘yan fashi, ta’addanci, wariyar launin fata, da satar mai, na bukatar wani sabon salon da ya haɗa da kara yawan jami’an tsaro.

KU KUMA KARANTA:Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gudanar da taron gaggawa kan barazanar tsaro a birnin Abuja

“Dole ne adadin ya canza kuma gwamnatin Bola Tinubu ta riga ta yi wani tsari wanda aka sanya a cikin shirinmu na magance wannan, za mu ƙara yawan adadin sojojin Najeriya, za mu kara kaimi ba kawai adadin ba,da horo da kayan aiki,” in ji gwamnan Kaduna.

A nasa ɓangaren, Alake ya amsa tambayar kan yadda Tinubu ke shirin fitar da ‘yan Najeriya daga ƙangin talauci idan aka zaɓe shi da kuma daƙile satar mai cikin watanni shida.
“Babban manufarsa na bunƙasa ci gaban tattalin arziki shine, baiwa kamfanoni masubzaman kansu damar yin jarin da za su ƙara yawan aiki, bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da kuma rage talauci,” in ji shi.

Har ila yau, Gbajabiamila ya amsa tambaya kan dabarun Tinubu kan tsaro, shugabar mata na jam’iyyar APC a matakin ƙasa ta amsa tambaya kan batun kiwon lafiya, da yadda za a mayar da magudanar kwakwalwa zuwa riba ga kasa da dai sauransu.

1 COMMENT

Leave a Reply