Sanarwar: Gwamnatin tarayya ta ba da umarnin rufe FGC Kwali, cikin matakan tsaurara tsaro a Kwalejojin Unity

0
193

Ma’aikatar Ilimi ta tarayya ta bayar da umarnin rufe ɗaya daga cikin kwalejojin nan take, wato Kwalejin Gwamnatin tarayya da ke Kwali, a ƙaramar hukumar Kwali a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, wanda ya bayar da wannan umarni da sanyin safiyar yau, ya ce rufewar ya zama dole sakamakon taɓarɓarewar tsaro da aka samu a ƙauyukan Sheda da Lambata, da ke wajen ƙaramar hukumar Kwali, wanda kuma hakan barazana ne ga FGC Kwali.

A cewar Ministan, shiga tsakani da hukumomin tsaro suka yi a kan lokaci ne ya ceci lamarin. Adamu Adamu ya kuma bayar da umarnin a shirya yadda ɗaliban shekarar karshe za su kammala jarabawar NECO.

Ministan ya kuma umurci shugabannin kwalejojin Unity a faɗin ƙasar nan da su haɗa kai da hukumomin tsaro da ke yankunansu, domin daƙile duk wata taɓarɓarewar tsaro a makarantunmu.

Ben. Bem Goong, Daraktan Yaɗa labarai da hulda da Jama’a.

Leave a Reply