Rikicin APC A Kano: ‘Yan Gandujiyya Sun Mayar Wa Su Shekarau Martani

0
506

Daga Wakilinmu

Gwamna Ganduje da Sanata Shekarau

Ɓangaren  jam`iyyar APC da gwamna Kano ke jagoranta ya ce a shirye yake ya yi tafiya da ɓangaren Senata Ibrahim Shekarau ba tare da nuna wani bambanci ba.

Hakan ya biyo bayan matakin kotun daukaka kara a Abuja ta tabbatar wa bangaren Gandujen shugabancin jam’iyya, inda uwar jam`iyyar ba ta yi jinkiri ba wajen bai wa bangaren shaidar shugabanci a jihar Kano.

Bangaren Senata Shekarau dai ya nuna rashin jin dadinsa game da wannan matakin da kuma wadansu kalamai da suke ce gwamna Ganduje ya yi, wadanda suke zargin cewa babu dattako a ciki.

To amma Honarabul Kabiru Alhassan Rurum, dan majalisar wakilai kuma daya daga cikin jiga-jigan ɓangaren gwamna Ganduje ya shaidawa BBC cewa su fatansu shi ne ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau ya manta da komai su koma tamkar yadda suke a baya, wato a gudu tare a tsira tare.

”Dukkanin mu uwa daya uba daya muke, ‘ya’yan jam’iyya daya ne illa sabani da ya zo da rashin fahimta kuma wannan ba zai hana mu sake zama mu ci gaba da tattaunawa ba.

Fatana shi ne da mu da mu kai nasara da su da sukai akasin hakan mu hada kai kamar yadda muka hada kai 2019, domin ko babu komai jam’iyyar mu daya kuma dukkaninsu shugabannin mu ne.

Mu na ganin lallai lokaci ya yi da ya kamata mu hada kai, a yafi juna kuma a gudu tare a tsira tare,” in ji Rurum.

Ya ce ko da yake a baya an yi maganganun da ba su yi wa ɓangaren sanata Shekarau dadi ba, amma magana zarar bunu ce murna da shauki da annushuwa ne suka sanya gwamna Ganduje fadar maganar da ake zargin ya fada din.

Rurum ya kara da cewa, amma a bayyani na biyu lokacin da suka je karbar satifiket na shugaban jam’iyya, ya yi jawabin da kira a gare su da su yi hakuri, su zo ayi tafiyar nan tare.

Ya kuma ce gwamnan a shirye ya ke ya sake nemansu domin a ci gaba da tattaunawa don hada kai kamar yadda ake a baya.

Kan batun da bangaren Sanata Shekarau ke yi na ganin uwar jam’iyya ba ta yi adalci ba Rurum ya ce: ”mu masu biyayya ne da hukuncin kotu da uwar jam’iyya ko ya yi dadi ko bai yi ba, sanna ita jam’iyya ita ce ta san dalilin da ya sanya ta dauki wannan matakin dan haka hakkin ta ne ta yi bayanin dalilin da ya sa su daukar wannan hukuncin”.

Ɓangaren da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta na jam’iyyar APC a Kano ya ce za su tafi Kotun Koli don ci gaba da kalubalantar bangaren su Gwamna Ganduje a rikicin shugabancin jam’iyyar da su ke yi.

Tsohon gwamnan Kanon ya kuma nuna rashin jin dadinsa da wasu kalmomin batanci da ya ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi amfani da su jim kadan bayan hukuncin kotu da ke cewa bangaren gwamnan ke da halastaccen shugaba.

A ranar Alhamis ne dai kotun daukaka kara ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar ga Abdullahi Abbas, kuma sa’o’i da yanke wannan hukuncin uwar jam’iyya ta kasa ta mika masa takardar shaidar shugabanci, matakin da bai yi wa ɓangaren Shekarau dadi ba.

A tattaunawarsa da BBC Hausa, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce uwar jam’iyya ta nuna rashin adalci kuma sun yi mamakin irin kalaman da suka fito daga bakin Gwamna Abdullahi Ganduje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here