Rayuwar Ganimul Miftah: Izina da tausayi da ƙarfafa gwiwa

Daga Sheikh Umar Tijjani

GANIMUL MIFTAH shi ne yaron da ya buɗe karatu a filin wasan ƙwallon kafa na duniya wanda a yanzu haka yake wakana a Qatar, bayan ya gabatar da karatu ya ja hankalin duniya sosai kasancewar sa mai buƙata ta musamman, wannan ya sa aka shirya masa lecture ta musamman, lakcar tasa ta bar abubuwa masu muhimmanci na ƙarfafa gwiwa ga dukkan wanda yake nema ya ja da baya a rayuwa, tare da nuna ƙarfin iyaye da gudummarwasu akan ƙarfafa wa ƴa ƴa su gwiwa musamman iyaye mata.

Yayi bayanin tsangwama da ya samu kansa acikin al’umma, wanda tun yana yaro ba’a iya daukan sa saboda ƙan ƙanta da kuma tunanin wani abu zai taɓu a jikin sa, sannan duk Makarantar da aka kai shi iyaye ba sa yarda a ɗauke shi saboda kada ƴa ƴan su su dinga firgita, sunayen banza babu irin wanda ba a saka masa ba, an saka masa kwaɗo, kifi, maciji da sauran su, amma yace duk wannan abubuwa da ya dinga faruwa dashi mahaifiyarsa itace take ƙarfafa masa gwiwa.

Ya ƙara dacewa ita ta shirya masa yanda zai rayu acikin gida, sannan tayi masa makaranta ta musamman da take koya masa karatu duk acikin gida, yace kuma da yawa Allah yana jarrabar mutum da rauni amma kuma ya ba shi wata baiwa ta musamman, don haka shi an ba shi baiwa ta fahimta da ƙarfin ƙwaƙwalwa, mahaifiyarsa ita ce ta koya masa idan ya ga wani yana kallon sa kallon izgili yayi masa murmushi ya kuma tabbata yayi masa sallama.

Daga ƙarshe yayi nasara mai yawa; ya ce yau ga shi yana da kamfani da yake gudunarwa a matsayin shugaba (kamfanin ice cream) kimanin mutum sittin ke aiki a kamfanin, sannan ana gayyatarsa gabatar da lecture a kowane ɓangare na ƙasar subhanllah!

Sannan suna rabawa masu buƙata ta musamman irin kujeru masu motsi a kowane ɓangare a ƙasar kuma har yanzu abun yana cigaba.

Miftahu tare da babban jarumin Hollywood Morgan free man a taron buɗe ƙwallon ƙafar kofin Duniya, Qatar.

Yau ga shi duk duniya ta san shi, sautin karatunsa na Alƙurani ya shiga cikin sautuna na malaman ƘUR’ANI na duniya kuma ga yanayin da aka halicce shi da shi.

Lalai akwai IZINA da yawa iyaye mata ku ƙara dagewa wajen yiwa ƴa ƴan ku tarbiyya da ƙarfafa musu giwa da ba su “hope” a cikin rayuwa domin tarihi ya nuna irin malaman da kuka futar wanda duniya har yanzu tana alfahari da su.

Kada ka taɓa karaya a rayuwa da ƙoƙari da jajircewa abun da ba zai yiwu ba yana komawa mai yuwuwa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *