Nuhu Abdullah: Ƙwazonsa da yawan dukiyarsa

0
535

Nuhu Abdullahi ɗaya ne daga cikin fitattun jaruman da ke da hazaƙa a masana’artar fim ta Kannywood.

Kyawunsa, yadda yake tafiyar da rayuwarsa, da salon wasan kwaikwayonsa zai sa ku so shi nan take, kuma hakan ne yasa yayi shura.

Ba sabon fuska bane a masana’antar, idan ka kalli fim ɗin hausa mai suna ”Labarina” to zaka fahimci Nuhu Abdullahi sosai.

Nuhu Abdullahi fitaccen jarumin kannywood ne, mai shirya fina-finai a Najeriya. Ya shahara da bajintar wasan kwaikwayo a fina-finan Hausa. An haife shi a Jihar Kano a Najeriya, a ranar 3 ga Janairun 1991.

Nuhu yayi karatunsa na firamare da sakandare kafin ya ci gaba da karatunsa a jami’a, Nuhu ya fara harkar fim ne tun a shekarar 2009 a matsayin furodusan fim kafin ya zama cikakken jarumi a Kannywood.

Ya shiga masana’antar ne bayan ya fara fitowa a wani fim mai suna “ƙanin Miji” wannan fim ya ba shi damar shahara a Najeriya.

Nuhu ya yi fice a fina-finai daban-daban kamar Aisha, Labarina, Taliko Ta Sani, Mugun Zama, Adon Gari, Miji Na, da dai sauransu.

A halin yanzu Nuhu Abdullahi yana auren kyakkyawar matarsa ​​mai suna Jamila Abdulnasir. Anyi auren Nuhu Abdullahi a ranar Asabar 4 ga watan 2020. Auren sa ya kasance ɗaya daga cikin mafi kyau da shahara a Kannywood.

An ƙiyasta dukiyar Nuhu Abdullahi da ta kai kusan dalar Amurka $400,000 a shekarar 2020.

Ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa a Kannywood a gasar City People Entertainment Awards a shekarar 2015, an zaɓe shi a shekarar 2016 Africa Magic Viewers Choice Awards a mafi kyawun shirin fim na asali, sannan kuma an zaɓe shi a 2017 Africa Magic Viewers Choice Awards.

Zai iya dacewa da duk wani ‘role’ da aka ba shi kuma salon wasansa yana da matukar ƙayatarwa ga masoyansa da kuma masu sha’awar kallon fina-finai.

Leave a Reply