NAHCON ta sanar da kuɗin aikin Hajjin bana

2
362

Hukumar kula da aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON), ta sanar da farashin jigilar maniyyata aikin hajjin wannan shekarar ta 2023 zuwa ƙasar Saudiyya.

Shugaban Hukumar NAHCON ɗin, Zikrullah Hassan, ne ya sanar da sabon farashin kuɗin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja Ya ce kuɗin na bana bai zama bai ɗaya ba, kamar da, inda ya ce farashin ya bambanta da jihohi.

KU KUMA KARANTA: A watan Disamba Hukumar Alhazai zata fitar da adadin mutanen da za suyi aikin Hajjin 2023 a Najeriya

A cewarsa, dukkan mahajjacin da zai fito daga Maiduguri da Yola zai biya Naira miliyan biyu da dubu ɗari takwas da casa’in.

Mallam Hassan, ya ce mahajjatan da suka fito daga wasu jihohin Arewa za su biya Naira miliyan 2,919,000. Ga Jihohin Kudu maso Gabas da Kudu-maso-Kudu ban da Kuros Riba, maniyyatan da ke da niyyar biyan kuɗin aikin Hajji na Naira 2,968,000.

“Cross River yana da mafi ƙarancin farashi. Alhazan Kuros Riba masu niyyar zuwa Hajji za su biya Naira 2,943,000,” in ji shugaban.

Yayin da maniyyatan jihohin Ekiti da Ondo za su biya Naira miliyan biyu da dubu dari takwas da tamanin da takwas, yayin da maniyyatan jihohin Legas, Ogun da Oyo za su biya Naira miliyan 2,993,000 kowannensu.

Shugaban hukumar ta NAHCON ya ƙara da cewa ranar 24 ga watan Afrilu ne wa’adin kammala aikin Hajji, inda ya jaddada cewa ba za a samu ƙarin ranakun da za a yi ba.

2 COMMENTS

Leave a Reply