Na Shiga Hadarin Mutuwa Saboda Buhari – Nastura Ashiru Sharif

0
375

Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban kwamitin Amintattun gamayyar kungiyoyin matasan arewacin Nijeriya Dokta Nastura Ashiru Sherif, ya bayyana cewa a can baya ya shiga munanan hadurran mutuwa saboda ganin Buhari ya zama shugaban kasa da zaton za a gyara kasar baki daya.
Nastura Ashiru Sharif ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar Talbijin ta “Tambarin hausa” da ke da mazauninta a cikin garin Kano.
Nastura ya ci gaba da cewa a kokarin ganin Muhammadu Buhari ya zama shugaban Nijeriya a can baya “akwai lokacin da an kira ni a Kaduna mun gama tattaunawar da zamu yi ni da abokina muka kama hanyar Kano mun je garin Kwanar Dan Gora, sai muka ga ana yin fashi sai muka tsaya kamar yadda kowa ya tsaya wanda daga baya sai muka ga motoci na aron hanya suna tafiya ta bangare daya,mums sai muka bi kar yadda sauran jama’a suke yi, ashe canza wuri suka yi ta yadda da kazo sai kawar ka gansu a dai dai wani hawa a kan hanya, to,  Nike tuki sai kawai na canza na juya motar baki daya”, inji Nastura.
“Nan take kawai sai suka biyo mu da gudu muna tafiya sai kawai na taka motar da gudu na shiga wata hanya a lokacin marar kwalta da ta nufi wani kauye ashe su mutanen garin sun san yadda lamarin yake domin ana yawan tare hanyar, ni kuma sai na rufe fitilar motar nan da nan mutanen garin suka ce in shiga in ajiye motar a wani wuri sai muka fito muna kallon barayin nan suka yi harbe harbensu muka shiga wani masallaci wannan kenan”.
Sai kuma zamu je wayar wa da jama’a kai a dai dai garin Toro, muna cikin mota kirar Bus mai jan fenti Kawai sai muka ga jama’a suna yin taron wata jam’iyya daban da ta mu kafin ka ce me dukkan gilashin motar an zubar da su nan da nan aka fitar da mu daga cikin motar amma sai Allah ya rufa mana asiri da akwai wani dan Jihar Bauchi da jama’ar duk sun san shi sai dattawa suka taso suka ce muma hakika Buhari zamu zaba, wannan ne ya cece mu domin motarmu mun saki wakar Buhari rikon Najeriya sai mai gaskiya.
Akwai kuma wani misalin guda daya ” in da muka je wani taro a gidan Arewa cikin Kaduna muna wani taro amma aka turo wasu yan dabar siyasa suka tayar da mu,malaman addini da Limamai suka rika cika rigunansu da Iska su na rugawa domin yan dabar siyasa sun kawo hari a dakin taron da dai misalai da yawa duk a kan Buhari muka samu wadannan tsallake rijiyar da baya”.

Nastura ya kuma ce shi a matsayinsa na mutum daman can bai amince da batun karba karba ba domin da ka ce kada wasu su tsaya takara domin sun fito daga wani bangare na kasar nan to hakika an taka tsarin Dimokuradiyya domin ya ba kowa dama a tsarin tsayawa da zaben wanda mutum ke bukata.

Leave a Reply