A Kara Bunkasa Kwakwacin Dawanau-Inji Bala Na Sani

0
301

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

Shugaban kungiyar kanikawa na masana’antar gyaran ababen hawa ta Kwakwacin Dawanau, Alhaji Bala na Sani mai Kwakyara ya roki gwamnan jihar Kano Dokta  Abdullahi Umar Ganduje da  Shugaban majalisar Karamar hukumar Dawakin Tofa  Alhaji Ado Tambai Kwa da su hada hannu domin bunkasa wannan guri.

Yayi wannan kiran a zantawar su da wakilin mu, inda ya bayyana cewa masana’antar tana samar da aiyukan yi ga dubban al’uma musamman matasa don haka akwai bukatar ganin an samarda abubuwa muhimman domin bunkasa gurin duba da yadda ake zuwa gyaran ababen hawa har daga kasashe makwabta.

Bala na Sani ya kara da cewa gwamnatin Ganduje tana kokari sosai ta fuskar samar da aiyukan dogaro dakai ga al’umar jihar Kano, don haka yana dakyau a waiwayi wannan masana’anta mai tsohon tarihi musamman ganin yadda take daukar nauyin wani kaso na bada aikin yi ga dubban matasa  don magance zaman sauraro.

Yace” idan aka samar da wutar lantarki wadatacciya a  wannan  masana’anta ta Kwakwacin Dawanau da masallacin Juma’a da Kuma karamin asibitin Shan magani, ko shakka babu gurin zai kara samar da aiyukan yi ga mutane tareda bunkasa tattalin arzikin kasa da na al’uma cikin lokaci kankane”.

Haka Kuma maikwakyara ya sanar da cewa tuni Shugaban Karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa ya samar da babbar na’urr raba wutar lantarki watau “Transformer” Amma tana nan ajjiye ba’a sami damar hada ta ba, don haka suke rokon gwamnatin Kano da ta Karamar hukumar Dawakin Tofa da su taimaka wajen ganin an hada wannan wuta domin ci gaban masana’antar.

Dangane da batun samar da masallacin Juma’a a  da karamin asibiti  a wannan guri, shugaba Alhaji Bala na Sani ya bayyana cewa akwai mutane dubbai a wajen kuma duk ranar Juma’a sai sun yi tafiya zuwa garin Dawanau ko wasu guraren  suke yin sallah, treda fatan cewa za’a duba wannan kuka nasu da idon rahama.

A karshe, Bala na Sani Mai Kwakyara ya jinjinawa gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Shugaban Karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa da dukkanin mataimakan su saboda kokarin da suke yi na kyautata rayuwar al’uma.

Leave a Reply