Malam Garba Nayamma ya kwashe shekaru 56 yana tuƙa keken da ya saya a zamanin tsohohn shugaban ƙasar Najeriya, Yakubu Gowon.
“Na sayi wannan keken ne fam uku wato naira shida kenan kuma har yanzu sai dai kawai idan wani abu ya lalace na sauya.”
Malam Garba ya ce a tsawon shekarun nan da ya kwashe yana amfani da keken, da shi yake zuwa gona da ma duk wata ziyara da yake yi a garuruwan arewacin Najeriya.”
Duk yawon ‘yan matanci da muka yi da wannan keken muka yi shi. Na kan ɗauki abokaina domin zuwa zance inda nake ɗora ɗaya a gaba sannan ɗaya kuma a kan kariya.”
Ya ƙara da cewa a duk lokacin da aka dauke min wannan keken to lallai an taƙaice ni kasancewar shi ne abun hawana da na riga na sani. Duk da cewa malam Garba ya tsufa domin ya wuce shekara 70 da haihuwa amma da ƙwarinsa wataƙila saboda irin shekarun da ya kwashe yana tuƙa wannan keke wanda hakan motsa jiki ne.
“Ba ni da wata cutar da ke damu na.”, BBC HAUSA ta rawaito.