Muhimman abubuwa 9 gameda fasahar AI (Artificial Intelligence), daga Sadiq Tukur Gwarzo

  1. Artificial Intelligence itace gagarumar fasahar da wannan ƙarni ke tinƙaho da ita, fasahar na bayar da dama ga Kwamfuta ko mutum-mutuminta wajen aiwatar da wasu ayyuka masu buƙatar tunani da yanke hukunci gwargwadon bayanan da ake dasu tamkar dai yadda ɗan Adam yake yi (akwai bayanai aƙalla sama da gigabyte biliyan biyar a yanar gizo).
  2. Fasahar ChatGPT na kamfanin OpenAI ya zama mutum-mutumin farko da ke tallafawa dukkan mai neman sani game da abubuwa da yawa a wannan duniyar. Anan kusa, mutum-mutumin ya samu nasarar lashe jarrabawar zama likita a ƙasar Amurka wanda ke nuni da cewa anan kusa zata fara duba marasa lafiya, haka kuma an fara jarrabta aiki da ita wajen yin Alƙalanci a wasu kotuna.
  3. LAFIYA: An fara amfani da fasahar AI wajen gina ‘Super computers’ masu tallafawa likitoci gabatar da ayyukansu. A zuwa yanzu, akwai masarrafai da dama misalin ‘Healthtap’ da suke iya baiwa marasa lafiya shawarwarin lafiya ta yanar gizo gwargwadon abubuwan dake damunsu.
  4. ILIMI: Fasahar AI na tallafawa ƴan makaranta da gagarumin taimako; misalin shafin writesonic.com da workcraft.ai na AI na iya rubuta dumujin muƙala daga tsirarun kalmomi, shafin scribbr.com na bayar da zantukan malamai na ilimi ga masu bincike dangane da wata mas’ala, kickresume.com na rubutawa mutum takardar neman aiki, grammarly.com na duba ‘grammartical error’ da makamantansu.
  5. Kamfanin Google ya soma jarabta nasa mutum-mutumin mai suna ‘Aprentice Bard’ wanda zai yi gogayya da ChatGPT kasancewar kamfanonin duniya duk sun rungumi wannan fasaha ta AI.
  6. Fasahar AI na da alaƙa da raguwar ayyukan yi ga ma’aikata. A shekarar 2022 da ta gabata, kamfanonin Tesla, da Google, da Amazon, da Microsoftda walmsun su duk sun rage ma’aikata wanda ake dangantashi da bijirowar fasahar da zata iya aikin mutane sama da 1000 a ƙanƙanin lokaci.
  7. ZIRGA-ZIRGA: Tun da jimawa aka soma samar da motoci masu tuƙa kawunansu daga fasahar AI. Waɗannan motoci suna da basirar kaucewa hatsarurruka, da yin amfani da taswirar birane wajen kurɗawa zuwa duk inda aka umarce su. Kamfanin Tesla shine kan gaba wajen samar da irin waɗannan motoci. Amma dai ana cigaba da gwajin su kafin sahalewa mutane amfani dasu akai-akai.
  8. TSARO: Ana amfani da wannan fasahar wajen samar da tsaro walau ta sigar kyamarorin CCTV ko ta ƙirƙirar mutum-mutumin da yake iya gane abu mai hatsari tare da ɗaukar matakinajansa gwargwadon umarnin da aka bashi.
  9. NISHAƊI DA KASUWANCI: Ana amfani da fasahar AI wajen samar da hotuna da bidiyoyi na abubuwa masu yawa, abinda kawai fasahar ke buƙata shine a bata bayanan waɗanda ake son ta samar da hotunansu. Akwai masarrafai da dama masu iya yin wannan aiki misalin synthesia.

Hakanan manyan kamfanoni suna amfani da wannan fasahar wajen tantance bayanan mutane a kafafen sadarwa tare da gano abubuwan da suka fi so gami da bunƙasa kasuwancinsu daga waɗannan bayanai.

Babban abu dai shine; muna iya cewa fasahar AI ta shiga kusan ɗaukacin fannonin rayuwar ɗan Adam, don haka ko dai mutum ya koyi hanyar cin gajiyarta, ko kuwa yana ji yana gani zata raba shi da hanyar cin abincinsa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *