Gwamnatin Najeriya za ta fara amfani da kimiyyar zamani wajen fuskantar ‘yan bindiga

0
107

Ganin yadda matsalolin tsaro suka ƙi ci, su ka ƙi cinyewa ya sa gwamnatin Najeriya shan alwashin sauya salo ta hanyar amfani da kimiyyar zamani wajen fuskantar ‘yan-bindiga da sauran masu laifuffuka don magance matsalar tsaro baki ɗaya.
Ministan tsaro a Najeriya, Malam Mohammad Badaru Abubakar wanda ya halarci taron bita ga malaman addinin Musulunci a garin Kaduna yau Talata ya ce nasara kan yaƙi da ‘yan-sari-ka-noƙe na da matuƙar wuya.

Maganar matsalar tsaro da tsadar rayuwa dai sune manyan batutuwan da majalissar ƙoli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya ta jawo hankalin kenan a wajen wannan taro, shi yasa ministan tsaron Najeriya Malam Mohammad Badaru Abubakar ya bayyana matakan da gwamnatin tarayya ke dauka don murƙushe matsalar baki ɗaya.

Ya ce yanzu da zaran ‘yan-bindiga sun fito kafin su gama kai hari su koma daji jami’an tsaro sun gama da su ta hanyar gano inda su ke da kuma ɗaukar matakin tarwatsasu.

To shin ko gwamnatin Najeriya za ta iya amfani da kimiyyar zamani don murƙushe matsalar tsaro kamar yadda wasu jami’an ta su ka dinga iƙirarin a baya, wannan ce tambayar da Muryar Amurka ta yi wa masanin harkokin tsaro Manjo Yahaya Shinko mai-ritaya wanda ya ce idan har da gaske gwamnatin tarayya za ta yi amfani da kimiyyar zamanin abu ne mai yiwuwa sai dai kuma ya ce gwamnatin ta daɗe ta na makamantan wadannan alƙawura ba tare da an gani a ƙasa ba.

KU KUMA KARANTA:’Yan fashi sun kai hari bankuna da ofishin ’yan sanda a Kogi

Kafin maganar amfani da kimiyyar zamani, gwamnatin tarayya ta sha alwashin ƙirƙiro ‘yan-sandan jihohi don tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya, sai dai kuma babban sakataren majalissar ƙoli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya, Malam Nafi’u Baba Ahmed ya ce dole gwamnati ta taka a hankali.

Baba Ahmed ya ce gwamnoni za su iya amfani da ‘yan-sandan jihohi wajen musgunawa ‘yan-adawa da kuma karya ƙa’idojin aikin tsaron da ka iya zama matsala ga ƙasa.

Tuni dai ganin jan-ƙafar da ake ta samu kan kirkiro rundunar ‘yan-sandan jihohi ya sa wasu yankuna da kuma ɗaiɗaikun jihohin ƙirƙiro rundunonin da ke aikin agaza wa tsaro, sai dai duk da haka ba a daina samun matsalolin tsaron a waɗannan jihohi da kuma yankuna ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here