Daga Fatima GIMBA, Abuja
Wadannan ‘yan kananan halittu wadanda ido ba ya iya ganinsu, suna rayuwa ne a galibi inda yake da kusanci da raba ko ruwa musamman inda iska ba ta shiga ta fita, sannan kuma hasken rana ba ya ratsawa, in ji masana.
Wannan yanayi inda wadannan ‚yan mitsimitsin halittu ke rayuwa shi ne suke rubar da abubuwa da ake iya gani ya jikin bango ko litattafai ko tufafi, inda za a ji har daki ko wurin da kayan suke yake wari.
Me ke janyo ruma?
Haka kuma za a iya cewa ruma danshi ne a killataccen wuri da zai iya kasancewa daki ne ko wata akwatu ko wani wurin ajiye abu, inda sakamakon yanayi musamman na damuna ya kansa danshi da yake cikin iska ya haifar da wannan ruma.
Lokacin damuna shi ne lokacin da aka fi samun danshi a cikin iska, wannan ne ya sa a lokacin aka fi samun ruma.
Sannan kusancn wuri da ruwa ko da ba a lokacin damuna ba ne, misali idan daki ko gini yana kusa da inda ruwa yake ana samun ruma a wurin.
Kamar magudanar ruwa ko famfo ya fashe ko wata rijiya ko kuma wurin da aka yi ginin wuri ne mai dausayi, duka wadannan suna kara haddasa ruwa, muddin babu iska wadatacciya da hasken rana a wannan killataccen wuri.
Illar ruma ga lafiyar mutum
Ruma tana haifar da illoli da dama kama daga na muhalli zuwa ga kayayyaki da ma lafiyar mutane.
A bangaren lafiya ruma tana da illa musamman ga mutanen da suke da kan-jiki domin ta kan janyo wasu mutanen masu irin wannan larura jikinsu ya rika kaikayi har ma kuraje su fito a jikinsu, kamar yadda Dakta Ibrahim Mijinyawa, wani likita a Abuja ya yi wa BBC bayani.
Likitan ya ce, yanayin yana kuma iya shafar ido ta yadda za a ga idanuwan mutum na yin ja sannan ga kaikayi da ruwa,.
Wanda wannan duk matsala ce da ruma ko wannan danshi na damuna ko wurin da ruwa ke kwanciya ko makwabtaka ke yi ga lafiyar jikin mutum.
Haka kuma likitan ya ce akwai mutanen da wannan ruma ko danshi ke sa wa suna mura kusan kodayaushe a lokacin damuna ko kuma idan suka shake shi.
Sannan yanayin yakan iya tsananta wa wasu mutamnen da ke da larurar numfashi musamman asma ko mura ko kuma tari.
Likitan ya ce ga masu irin wannan matsala ta numfashi, hanyar da suke shakar numfashi ka iya toshewa, wanda idan ba a yi sauri na ba su magani ba, matsalar ka iya kai su ga rasa rai.