Mazauna Kano sun yi ƙira da Gwamnatin tarayya wajen kawo ƙarshen cutar zazzaɓin cizon sauro

0
415
Mazauna Kano sun yi ƙira da Gwamnatin tarayya wajen kawo ƙarshen cutar zazzaɓin cizon sauro

Mazauna Kano sun yi ƙira da Gwamnatin tarayya wajen kawo ƙarshen cutar zazzaɓin cizon sauro

Daga Jamilu Lawan Yakasai

A lokacin da Majalisar dinki duniya ke bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro, a gefe guda kuma Mazauna Jihar Kano na kokawa dangane da yawaita sauro. Wanda ke haddasa cutar Malaria.

Sakamakon wannan rana da aka ware wakilin Jaridar Neptune Prime ya ziyarci Unguwar Gandun Albasa, da ke yankin karamar hukumar birnin Kano. Sai dai wani mazaunin unguwar mai suna Isma’il yace shi babu wani cigaba da ya gani na yaki da cutar zazzabin cizon sauro, sakamakon kullum abun kara yawa yake, ya kara da cewar a hanyu haka yaransa Biyu duk suna fama da cutar Malaria.

Malama Maryam wacce ta fito daga chemist anyi mata allurar malaria, tace duk da shiga gidan sauro “Net” da take yawan yi hakan bai hanata zazzabin cizon sauron ba, tace Gwamnatin Jiha data Tarayya su kawo wa jama’ar Kano dauki domin magance sauro a fadin Jihar.

KU KUMA KARANTA:Direban mota ya kashe jami’in Karota a Kano

Jihar Kano gudace daga cikin mafiya yawan al’umma a arewancin Najeriya, kuma tana daya daga cikin wanda ke fama da barazanar zazzabin cizon sauro.

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta bayyana haka ne a lokacin da ake tsaka bakin ranar wayar da kan jama’a kan yaƙi da cutar Zazzaɓin cizon sauro ta Duniya, da majalisar dinkin Duniya ta ware ranar 25 ga watan Afrilun kowacce shekara domin bikin ranar.

Yankin kudu da hamadar Sahara a Afirka ne ke da kaso mafi yawa na masu fama da Zazzaɓin cizon sauron, inda a Najeriya cutar zazzabin cizon sauro ta zama kan gaba wajan hallaka mutane musamman yara ‘yan kasa da shekaru biyar.

Kamata ya yi al’umma su runga bin shawarar masana kiwon lafiya, wajen kula da muhallin su da sauransu.

Leave a Reply