Direban mota ya kashe jami’in Karota a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ta KAROTA, a Kano, Abubakar Ibrahim Shadaɗa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa Jaridar Neptune Prime a ranar Alhamis.
Hukumar ta ce, daga cikin waɗanda ake zargi har da wani jami’in soja da direban motar da kuma yaron sa.
Read also:Hukumar KAROTA a Kano ta gargaɗi masu kai wa jami’anta farmaki
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ya ce a daren jiya Laraba ne jami’an Hukumar KAROTA, suka kama wani Direban motar fakas (Container) da ake zargin sa da sanadiyar rasa ran wani Jami’n Hukumar a jihar mai suna Yahaya Barista, a lokacin da yake gudanar da aikin sa.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan, bayan da hukumar ta KAROTA ta ce ba zata lamunci cin zarafin da al’umma ke yiwa jami’anta a yayin da suke tsaka da aiki ba.