Mawallafin Neptune Prime zai ƙaddamar da asibitin cutar kansa, makaranta, da gidauniyar tallafi a Yobe

0
83
Mawallafin Neptune Prime, zai ƙaddamar da asibitin cutar kansa, makaranta, da gidauniyar tallafi a Yobe

Mawallafin Neptune Prime zai ƙaddamar da asibitin cutar kansa, makaranta, da gidauniyar tallafi a Yobe

Daga Idris Umar, Zariya

Dakta Hassan Gimba, mai wallafa jaridar Neptune Prime (English) da Neptune Prima (Hausa), zai ƙaddamar da wasu manyan ayyuka guda uku a jihar Yobe, wanda zai kasance daidai da bikin auren ɗansa, a ƙarshen makon nan, a garin Potiskum.

Ayyukan sun haɗa da makarantar Hafsatu Gimba Ahmed Memorial, wadda aka sadaukar domin tunawa da mahaifiyarsa, kuma an kafa makarantar domin taimaka wa al’umma wajen samun ilimi.

Haka zalika, an kafa Gidauniyar Abubakar Monja Lifeline domin tallafa Matasa da koyon sana’o,in hannu irin su Fulambin, Ɗinki da sauransu.

Dakta Gimba ya kuma gayyaci baƙi don duba aikin gina Asibitin Lami Fatima Babare Cancer Outreach, wanda ke ƙarƙashin gidauniyar Lami Fatima Babare Cervical Cancer Foundation, domin tunawa da marigayiya matarsa, domin samar da ayyukan kiwon lafiya da tura masu fama da cutar kansa.

KU KUMA KARANTA: Mahaifin Daraktan Neptune Prime, Aisha Auyo, ya rasu

Za a gudanar da tarukan ne a ranar 31 ga Agusta, inda za a fara da bikin ɗaurin auren ɗansa da misalin ƙarfe 11:00 na safe a gidan Mohammed Babate, sannan a ƙaddamar da makarantar tare da gabatar da shirin tallafa wa gidauniyar. Za a ƙaddamar da waɗannan muhimman ayyukan ne a unguwar Jaji da ke cikin garin Potiskum jihar, Yobe.

Leave a Reply