Gwamnatin Gombe ta yi wa Almajirai 1,000 rajistar inshorar lafiya

0
68
Gwamnatin Gombe ta yi wa Almajirai 1,000 rajistar inshorar lafiya

Gwamnatin Gombe ta yi wa Almajirai 1,000 rajistar inshorar lafiya

Gwamnatin Gombe ta yi wa ɗaliban makarantun tsangaya fiye da 1,000 rajista domin duba lafiyarsu kyauta a ƙarƙashin shirin inshorar lafiya ta jihar.

An yi wa Almajiran rajista ne a wani ɓangare na samar da isasshen kiwon lafiya ga ƙananan yara masu ƙaramin ƙarfi a jihar.

Da yake ƙaddamar da shirin, wanda ofishin Mashawarcin Gwamna kan Makarantun Tsangaya, ya shirya, Mataimakin Gwamnan, Dokta Manassah Jatau ya jaddada aniyar Gwamnatin na inganta kuka da lafiyar ƙananan yara da masu ƙaramin ƙarfi.

Ya ce nan gaba jihar za ta ƙaddamar da tsarin kula da lafiya na tafi-da-gidanka mai suna GoHealth domin waɗanda ba su da ƙarfin zuwa asibiti su samu sauƙi.

KU KUMA KARANTA: An kuɓutar da almajirai 18 da ‘yan bindiga suka sace a Sakkwato

“Idan babu irin waɗannan tsare-tsare mutane da yawa ba za su iya kula da lafiyarsu ba, saboda su masu ƙaramin ƙarfi ne.

“Shi ya sa a yau muka ƙaddamar da yin rajistar almajirai 1,000 a ƙarƙashin shirin inshorar lafiya na jihar Gombe.”

Dr. Jatau ya bayyana kasancewar almajirai ƙananan yara masu ƙaramin ƙarfi da kuma yadda suke fuskantar barazanar kamuwa da ƙwayoyin cuta ya sa shirin ya ka ba su muhimmanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here