Mataimakiyar Gwamnan Kaduna Ta Nemi Hadin Kai Da Goyon Bayan Kungiyar NUJ

0
356

Daga; USMAN NASIDI. Kaduna.

MATAIMAKIYAR Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta bukaci hadin kai da ‘yan Jaridu a Jihar Kaduna domin samun hadin kai a fannin yada labarai.

Balarabe, ta yi wannan roko ne a ranar Alhamis yayin da ta karbi tawagar shugabannin kungiyar ‘yan Jarida ta kasa (NUJ), reshen Jihar Kaduna a gidan gwamnati da ke Kaduna.

Ta ce, kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da irin rawar da ‘yan jarida ke takawa, inda ta kara da cewa, “muna bukatar samun matsaya guda domin na san kuna da tashoshi da hanyoyin sadarwa da za ku iya kaiwa ga ci.

“Muna so mu sami irin wannan haɗin gwiwa wanda ke taimaka mana mu ba da bayanai masu dacewa, tabbatacce kuma tabbatacce ga jama’a,” in ji ta.

Mataimakiyar Gwamnan, ta ci gaba da cewa gwamnatin Jihar na da shirye-shirye da dama da suke ci gaba da gudana musamman a fannin bunkasa rayuwar bil’adama amma ta na mai bakin cinkin yadda mutane ba su da masaniya saboda karancin bayanai.

Ta yi nuni da cewar, yada bayanai da ya dace ga al’umma zai taimaka matuka wajen inganta arziki da samar da ayyukan yi da kuma ilimi.

“Misali mun ce ilimi a Jihar Kaduna shekaru goma sha biyu kyauta ne amma mutane sun sani,?” Ta tambaya.

Balarabe ta bukaci ‘yan Jaridu da su kasance masu bayyana haƙiƙanin gaskiya a cikin rahotonsu.

Tun da farko, shugabar kungiyar ta NUJ reshen Jihar Kaduna, Hajiya Asma’u Halilu a nata jawabin ta bayyana cewa NUJ ta kasance mai ruwa da tsaki a harkar samar da shugabanci na gari.

Sai dai ta yaba da kokarin gwamnati musamman a fannin ilimi, ci gaban matasa, tsaro da lafiya.

“Muna sane da cewa gwamnati ta amince da Naira miliyan 250 a shekarar da ta gabata don taimaka wa mata wajen haihuwa, wannan abu ne da ba a taba ganin irinsa ba domin babu wata Jihar da ta ware wani abu makamancin haka a baya a Najeriya,” inji ta.

Don haka ta bukaci gwamnati da ta yi la’akari da horar da ‘yan jarida a Kaduna, inda ta ce hakan zai yi matukar tasiri ga mambobinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here