Masu garkuwa sun sace matasa 21, har da budurwa da ke aikin tara kuɗin aurenta

Sace matasa 21 da ‘yan ta’adda suka yi a wata gona da ke kusa da ƙauyen kamfanin Mai ‘Yardua da ke ƙaramar hukumar Faskari a Jihar Katsina a ranar 30 ga Oktoba, 2022, ya jefa mazauna yankin cikin fargaba.

Da yake magana game da sace ‘yan matan, wani mai suna Muntari Auwalu ya ce ‘yar wansa na ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa. Mutumin mai tuƙa babur ne a Katsina, ya ce an kira shi ne a ranar Lahadi da daddare cewa an yi garkuwa da ‘yar wansa mai suna Asiya tare da wasu ‘yan mata a rana tsaka a lokacin da suke a gona.

Ya ce a ranar Laraba ana ƙoƙarin samo hanyoyin neman kuɗin fansa da ‘yan ta’addan ke nema a kan waɗanda suka yi garkuwa da su. Auwalu, wanda bai bayyana adadin kudin ba, ya ce, “da tsakar daren ranar Lahadi aka kira ni cewa an yi garkuwa da Asiya, kuma har yanzu ‘yan ta’addan ba su kai da gaya mana abin da suke bukata ba.

“Asiya tana shirin bikinta. Ina tsammanin hakan ya sa ta je ta yi aikin gona domin ta sami kuɗin bikin, amma aka sace ta. ” Yanzu haka a Katsina na ke zaune ina tuƙa babur na acaɓa ina kuma taɓa kasuwanci tunda ‘yan ta’adda sun hana mu komawa gonakinmu a Mairuwa.”

Ina tuntuɓar gida kowace rana kuma kamar yadda a safiyar jiya Larabar an faɗa mani cewa ‘yan ta’addar sun bayyana buƙatunsu yayin da aka nemi na bayar da nawa gudummawar. “Ba zan iya gaya muku adadin kuɗin ba kasancewar mutanenmu a gida ne suke da gaskiyar ƙididdigar, kira na ga gwamnati da ta inganta tsaro a cikin a yankin.”

Ni da wasu da dama daga ƙauyen Mairuwa muka ƙaura saboda ‘yan ta’addan” inji shi.Mazauna yankin sun ce ‘yan ta’addan sun kewaye gonakin ne da misalin karfe 3 na yammacin ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, 2022, a lokacin da matasan ke aikin girbin amfanin gona a gona.An ce an ɗauki matasan ne a matsayin leburori daga al’ummomin da ke kewaye da gonar, inda aka ce yawancinsu ‘yan ƙauyen Mairuwa ne.

Jerin sunayen waɗanda abin ya shafa da rundunar ‘yan sandan Katsina ta bayar ya nuna cewa akwai ‘yan mata a ƙalla bakwai a cikinsu. Lissafin ya kuma nuna cewa waɗanda aka kashen ‘yan t shekaru 16 zuwa 21, haka zalika sunayen waɗanda abin ya shafa kamar yadda aka samu daga rundunar ‘yan sandan su ne Lawal, mai shekaru 18, sai Mandiya ‘yar shekara 18 da Bilkisu ita ma mai shekaru 18 sai Samaila ɗan shekara 16 da Awanu shima mai shekaru 16, sai Dalha mai shekaru 21 da kuma Umeh Abdullahi ‘yar shekara 18 da Hadiza mai shekaru 17, sai Ibrahim Dalha mai shekaru 17, da Zainab ‘yar shekara 17 da Aliyu Baba mai shekaru 15 da Yusufu Dana shima mai shekaru 15.Sauran su ne Abdullahi mai shekaru 18, da Samaila, mai shekaru 18, sai Shehu mai shekaru 17, Asiya Abdul mai shekaru 19 sai Zuwaira mai shekaru 16 da Abdullahi mai shekaru 17, Amina ‘yar shekara 18 da Sani ɗan shekara 15 sai Nafiu mai shekaru 17.

Mazauna yankin sun kuma ce mai gonar da aka yi garkuwa da yaran yana zaune ne a Funtuwa kuma yakan ziyarci gonakin ne kawai a wasu lokuta. An kuma yi zargin cewa a baya mai gonar ya bai wa ‘yan ta’addan Naira miliyan ɗaya domin ya girbe amfanin gonarsa ba tare da an yi musu fyade ko kuma sace masu yi masa aiki a gonar ba, sai dai babu wanda zai iya tabbatar da hakan duk da haka.

Haka kuma, wani mutum da aka ce shi ne manajan gonar ba a iya gano shi a ranar Laraba ba. Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa an yi garkuwa da matasa 21. Ya ce, “An yi garkuwa da matasan ne a ranar 30 ga Satumba, 2022, da rana, amma rahoton faruwar lamarin ya kai ga ‘yan sanda da karfe 7.40 da yamma.”Waɗanda aka yi garkuwa da su 21 ne. Tun daga wannan lokacin, muna ta ƙoƙarin ganin an ceto su, duk lokacin da aka samu sabon ci gaba, zan sanar da ku.”

Bamu samu jin ta bakin mai baiwa gwamna Aminu Masari shawara kan harkokin tsaro ba, Ahmad Katsina domin jin ta bakinsa duk da cewa tuni jihar ta hada kai da jami’an tsaro domin ceto yaran. A halin da ake ciki kuma, a ranar Larabar da ta gabata an samu rahotannin cewa barayin na neman Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansa.


Comments

2 responses to “Masu garkuwa sun sace matasa 21, har da budurwa da ke aikin tara kuɗin aurenta”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Masu garkuwa sun sace matasa 21, har da budurwa da ke aikin tara kuɗin aurenta […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Masu garkuwa sun sace matasa 21, har da budurwa da ke aikin tara kuɗin aurenta […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *