Yadda ‘Yar Najeriya ta zama Janar a Rundunar Sojin Amurka

1
346

Wata mata ‘yar asalin Najeriya, Amanda Azubuike, ta samu ƙarin girma daga Laftanar Kanar zuwa Birgediya Janar na Sojojin Amurka a wani sansanin soji da ke Fort Knox a jihar Kentucky ta Amurka.

An haife ta a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, iyayenta ‘yan Najeriya ne. Azubuike ta shiga aikin sojan Amurka a shekarar 1994, kuma ta zama ma’aikaciyar jirgin sama bayan ta yi karatu tare da samun horo na farko Kwalejin Sojan Jiragen Sama.

Da yake tsokaci game da halayenta na jagoranci, Kwamandan Rundunar Sojojin Amurka, Janar James Rainey, ya bayyana cewa Azubuike ta kasance mai kyawawan halayyar da nagarta, domin don wanda yayi aiki tare da ita zai iya tabbatar da hakan.

” Bayan aikinta na zirga-zirgar jiragen sama, wanda ya dauki shekaru 11, ta ci gaba da aikinta na soja a matsayin jami’ar hulda da jama’a.

Azubuike a halin yanzu tana aiki a matsayin mataimakiyar kwamanda a Rundunar Kadet na Sojojin Amurka, kuma a baya ta taɓa zama Babban Hafsan Hafsoshi/Babban Mashawarci na Soja a Ofishin Sakataren Tsaro.

Ta kuma kasance Shugabar Hulɗa da Jama’a a Kudancin Amurka, yankin Fort Lauderdale, da Daraktan Hulda da Jama’a, Haɗin gwiwar Rundunar sojin birnin Washington.

Ta kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara a fannin sadarwa na Ƙungiyar ‘Yan Wasan Kwallon Kafa ta Ƙasa da kuma ma’aikatar Hulɗa da Jama’a na ƙungiyar NFL a Washington.

Baya ga cancantar ta aikin Soja, Janar Azubuike tana da digirin farko na Kimiyya a fannin aikin jarida da yaɗa labarai daga Jami’ar Central Arkansas.

Ta kuma kasance babbar jagora a fannin tsaro da nazarin dabaru daga kwalejin yakin sojan Amurka, sannan kuma ta yi jagora a fannin Ilimi da nazarin ƙwararru da hulɗa da Jama’a da kuma sadarwar kamfanoni daga Jami’ar Georgetown.

1 COMMENT

Leave a Reply