Wani ɗan Afirka ta Kudu da ya yi wata bajinta don kawai ya tabbatar da soyayyarsa ga masoyiyarsa.
Mutumin mai shekara 57, mai suna Joseph Kagiso Ndlovu, ya yi gudun kilomita 90 a wata gasar tsere ta ultra-marathon domin kawai ya nemi amincewar masoyiysarsa, Prudence.
An nuna shi riƙe da wata tuta inda a jiki aka rubuta saƙon da ke neman matar ta amince ta aure shi dai-dai lokacin da ya ke dab da kammala tseren.
“Prudence, za ki aure ni? Na yi gudun kilomita 90 saboda ke,” kamar yadda aka rubuta.
Kafafen yada labaran ƙasar da kuma wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta tsokaci kan labarin mutumin da ya yi wannan bajinta saboda so.