Marigayi Bashir Tofa Cikakken Dan Diokuradiyya Ne Da Kishin Kasa – Atiku Abubakar

0
327

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya kwatanta rasuwar tsohon dan takarar shugaban kasa Alhaji Bashir Tofa a matsayin babban rashi.

Da safiyar Litinin Bashir Tofa ya rasu bayan fama da ‘yar gajeruwar rashin lafiya a Kano.

Tuni dai an yi jana’izar marigayin a ranar Litinin a birnin na Kano.

“Marigayi Bashir Tofa cikakken dan Dimokuradiyya ne da kishin kasa. A kowanne lokaci yakan ba da gudunmowa da shawara akan al’umara da suka shafi wannan kasa.” Atiku ya ce cikin sanarwar.

“Tabbas wannan babban rashi ne. Ina Addu’ar Ubangiji Allah ya jikansa ya yafe masa. Allah ya ba shi gidan Aljanna. Ameen.” In ji Atiku.

Mariyagin ya tsaya takarar shugaban kasa ne karkashin jam’iyyar NRC a 1993 inda ya kara da dan takarar SDP MKO Abiola.

Abiola ya lashe zaben, amma gwamnatin mulkin soji karkashin Janar Ibrahim Babangida ta soke zaben.

‘Yan Najeriya da dama sun yi ittikafakin cewa zaben shi ne mafi sahihanci da kasar ta taba yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here