Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi maraba da sakin yara 21 da aka yi garkuwa da su

2
483

Majalisar Dinkin Duniya ta yi maraba da sakin yara 21 – mafi yawancinsu ‘yan mata, wadanda ‘yan bindiga suka sace a lokacin da suke aiki a wata gona a karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

A wata sanarwa da Asusun Kula da Kanan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar, ya ce labarin sakin yaran abu ne ”mai dadi”.

Sanarwar ta kara da cewa tun da farko ma bai kamata a sace yaran ba, tana mai cewa ”bai kamata a rika kame tare da farmakar kananan yara ba”.

KU KUMA KARANTA: Masu garkuwa sun sace matasa 21, har da budurwa da ke aikin tara kuɗin aurenta

UNICEF din ya kuma ce zai taimaka wa gwamnatin jihar Katsina wajen sauya wa yaran tunani.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan Sandan jihar Gambo Isa ya shaida wa BBC cewa shekarun yaran sun kama ne daga 15 zuwa 18. Kuma 17 daga cikinsu mata ne.

2 COMMENTS

Leave a Reply