Mai matakin karatun digiri yana sana’ar tuƙa Keke Napep

0
175

Daga Maryam Umar Abdullahi

Labarin wani bawan Allah mai suna Umar Ishaku

Tabbas na tausaya wa wani bawan Allah mai suna Umar Ishaku bisa ga halin da ya shiga duk da yana da matakin karatun digiri amma bai kashe zuciyarsa ya tsaya sai ya samu aikin gwamnati ba, sai ya kama sana’ar tuƙa Keke Napep domin ya rufawa kansa asiri, shi da iyalansa.

Ya haɗu da jarabawa, Keke Napep ɗinsa ta kama da wuta, nan ma bai zauna haka ba ya ci gaba da fafutuka domin rufa wa kansa asiri. Duk da yana ɗan taɓa Siyasa, amma kowa yasan halin ‘yan siyasar ƙasar nan, da yawa daga cikinsu babu burin taimakon wanda suke musu wahala sai dai kaɗan waɗanda Allah ya nufa.

KU KUMA KARANTA: An kama dattijai masu shekaru sama da sittin da zargin satar motoci

Muna roƙon Allah ya kawowa wannan bawan Allah mafita, Allah ya ba shi ikon cinye wannan jarabawar.

Idan akwai wanda yake da hanyar da zai taimaka masa da aikin gwamnati ko jari, to a taimaka masa don Allah.

‘Yan siyasarmu kuma kuji tsoron Allah, mutane suna muku ƙoƙari amma daga kunsamu dama daga ku sai ‘ya’yanku.

Leave a Reply