‘Mai buƙatar aikin soja a Amurka, ya Tuntuɓeni- Janar a Sojin Amurka yar Najeriya

0
519

Sabuwar Birgediya Janar ‘yar asalin Najeriya, Amanda Azuibike, ta miƙa takardar gayyata ga duk mai sha’awar shiga rundunar sojan Amurka da ya tuntuɓe ta.

Wannan babbar jami’ar sojan ta bayyana hakan ne a shafinta na Linkedin jim kaɗan bayan da aka samu labarin ƙarin girmar ta a yanar gizo.

A cewarta, akwai damammaki da dama a cikin sojojin Amurka ba tare da la’akari da da sana’ar mutum ko kwarewarsa ba. Ta ƙara da cewa, duk wanda ke son shiga rundunar ko ya san wanda yake so kada ya yi shakkar tuntubar ta da kansa.

“Ina jin daɗin yin hidima a cikin USl Army Cadet Command, da ba da gudummawa ga shugabannin sojojin mu na gaba. Muna da dama da yawa ga waɗanda ke da kyakkyawar manufa da rayuwa me ma’ana ga rundunar.Kamar yadda na gano tun a farkon rayuwa, Sojoji na da damammaki da dama, da bangarori yawa, kuma muna ba da dama da guraben karatu da yawa.”

KA/KI TUNTUƁE NI idan kai ko wanda ka sani yana son zama Hafsan Soja. Ko taya kuke ayyana nasara, Sojoji na iya taimaka muku isa wurin – muna son kasancewa cikin tafiyarku! ” ta rubuta.

KU

Ita ma da take magana kan tashi faɗin ta a rundunar sojin Amurka, Janar Azuibike ta ce ta samu damar shiga aikin sojan na Amurka a lokacin da ba ta kasance ‘yar kasar Amurka ba tukuna. Ta ƙara da cewa tana alfahari da al’adunta na Najeriya da tushenta kamar yadda take alfahari da kasancewarta Ba’amurkiya.

“Tafiyata ta musamman ce, kuma za ku iya koyan wani abu daga cikin jawabainda nayi, wanda daga zuciyata yake, “Na shiga sojan Amurka tun kafin na zama ‘yar ƙasar Amurka, a koyaushe inada yaƙinin cewa ƙasar nan mai daraja ce da girma. Ta cancanci a yi yaƙi dominta, kuma haƙika ita ƙasa ce mai damarmaki. Ina matukar alfahari da tushena, amma ni ma ina alfahari da kasancewa Ba-Amurkiya da kuma yin hidima a cikin mafi kyawun Sojoji a duniya!”

An haifi Amanda a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, iyayenta ‘yan Najeriya, kuma ta shiga aikin sojan Amurka a shekarar 1994 inda ta kai matsayin ma’aikaciyar jirgin sama bayan ta wuce Kwalejin Sojan Jiragen Sama na Basic Course.

Leave a Reply