Mahaifiyar Gwamnan Katsina Hajiya Safara’u ta rasu
Daga Idris Umar, Zariya
Inna LillaHi Wa Inna IlaiHi Raji’un
Allah Ya yi wa mahaifiyar gwamna Dikko Radda na jihar Katsina Hajiya Safara’u rasuwa sakamakon jinya da tayi.
KU KUMA KARANTA:Allah ya yiwa fitaccen attajiri a Kano Alhaji Nasiru Ahali rasuwa
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, marigayiyar ta rasu da asubahin yau Lahadi 23 March 2025 daidai da 23 Ramadan 1446
Allah Ya ji kanta Ya gafarta mata









