Allah ya yiwa fitaccen attajiri a Kano Alhaji Nasiru Ahali rasuwa

0
99
Allah ya yiwa fitaccen attajiri a Kano Alhaji Nasiru Ahali rasuwa

Allah ya yiwa fitaccen attajiri a Kano Alhaji Nasiru Ahali rasuwa

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Alhaji Nasiru Ahali, ya rasu a daren jiya Alhamis, bayan fama da jinya kamar yadda ɗansa, Aminu Ahali, ya sanar.

Marigayin mai shekara 108, shi ne shugaban kamfanin Mainsara & Sons, yana gudanar da harkar kasuwanci daban-daban, ciki har da buga littattafai da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje da kwangila da gina gidaje da aikin sarrafa ƙarfe da sauransu.

KU KUMA KARANTA:Gamayyar gwamnonin arewa sun yi alhinin rasuwar Sheikh Sa’eed Hassan Jingir

Anyi jana’izarsa a masallacin Jumu’a na Nasiru Ahali da ke Kurnar Asabe da ƙarfe 1 na rana a yau Juma’a.

Leave a Reply