Dole a binciki zargin lalata da Natasha ta yiwa Akpabio – Amnesty
Daga Ibraheem El-Tafseer
Amnesty International ta ce dole a binciki zargin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Goodwill Akpabio.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani kan rikicin da ke faruwa a majalisar dattawa.
KU KUMA KARANTA:Saboda na ƙi amincewa Akpabio ya yi lalata da ni, shi ne dalilin da ya sa ya tsane ni – Sanata Natasha
Cikin wata sanarwa da Amnesty International reshen Najeriya ta fitar, wanda Daraktan kungiyar, Isa Sanusi, ya sanya wa hannu, ya ce:
“Amnesty International na kira ga hukumomin Najeriya da su gaggauta gudanar da bincike mai zaman kansa, wanda ba na son rai ba, kan zargin cin zarafi ta fuskar lalata da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi wa Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio.