Daga Fatima Monja, Abuja
Mary Magdelene mai aikin zanece da ta kasance komai na jikinta ciko ne da roba. Da farko ta fara zuwa a mata filastik tiyata (plastic surgery) tana ‘yar shekara 21 domin tana so tafi kowacce mace girman mama a duniya.
Shikuma wannan aikin filastic tiyatan (plastic surgery) yana da jaraba (addiction) inji masu yi. Sunce “in kaje aka ƙara maka wani waje to sai ka koma domin a ƙara tado komaɗa da ciko.
Magdelene ta koma a karo na biyu domin a ƙara mata mazaunenta, bayan wasu lokuta mazaunen Magdelene da yai ma jikinta nauyi yakai robobin da aka mata ciko da su wani wajen ya fashe har ma yana fidda ruwa.
Duk da haka Magdelene bata daddara ba ta koma domin a kara mata girman laɓɓanta, da hanci da kuma girar ta. Ga waɗanda basu sani ba mu ‘yan Afrika da muke da manyan laɓɓa muke ganin kaman sunyi girma to su turawa har kuɗi suke zuwa su bada domin a cusa musu robot don ya ƙara girma.
Girma da yawan robbing ciko jikin Magdelene ya kai seda wani lokaci aka hanata shiga jirgi domin suna tunanin mutum ce ko mutum mutumin robace.
Sai dai abin dariya da ya faru da Magdelene bayan ƙara mata girman labba, sai ya kasance bakinta baya rufuwa.
Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.