Ma’aikatan wutar lantarki sun bi sahu, sun taya ASUU zanga-zanga

Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki sun yi shirin zanga-zangar nuna goyon baya ga ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU). Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta yi kira ga dukkan ma’aikata su fito domin nuna ƙin amincewa da ci gaban yajin aikin ASUU. Ƙungiyar ASUU ta shafe watanni sama da huɗu suna yajin aiki saboda wasu buƙatu da ta gabatarwa gwamnatin tarayya.

FCT, Abuja – Punch ta ruwaito cewa, ma’aikatan wutar lantarki a ƙarƙashin ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE), sun bi sahun ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC a zanga-zangar hadin gwiwa da ta shirya yi kan yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta umarci ma’aikata da su fito zanga-zanga a faɗin ƙasar nan a ranakun 26 da 27 ga watan Yuli domin nuna goyon bayansu ga yajin aikin da ASUU ta shiga.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *