Kuto ta yankewa Abduljabbar hukuncin kisa

Daga Shafaatu DAUDA, kano

Babbar kotun jihar kano ta yankewa Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kama shi da kalaman ɓatanci ga Annabi Mahammadu (S.A.W)

Alƙalin kotun mai Sharia Ibrahim Sarki Yola ne ya bayyana hukuncin a ranar Alhamis da da misalin ƙarfe 1:00pm na rana a kotun .

Sarki Yola ya ce bisa hujjojin da suka bayyana a gabansa na wanda ake ƙara, sannan kuma ya kasa kare kansa a bisa tuhumomin da ake mas, don haka ya yanke hukuncin kisan.

Sannan Abduljabbar abin da ake zargin sa da ya fada a cikin karatuttukansa kuma ya kasa kare kansa bisa kin nuna inda bayanin yake a littafi.

Ibrahim Sarki Yola ya ci gada cewa ya na mai umartar gwamnatin kano da ta rufe masallatan malamin guda biyu na As’habul khafi da Rasulun Ameen. dake filin mushe.

Kuma ya ce ya kwace littattafan Abduljabbar guda 189 da ya ke kafa hujja da su a wajen karatu.

Bugu da ƙari Alƙalin kotun ya hana yada karatun malamin a katafen sadarwa na Radio da na TV.

Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara na da damar ɗaukaka ƙara a babbar kotun ɗaukaka ƙara ta kano zuwa kwanaki 30 a cewar alkalin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *