Kotu ta tsare mai gidan haya kan lalata da ’yar shekara 6 a Ibadan

0
178

Wata Kotun Majistare da ke Iyaganku a Ibadan ta bayar da umarnin tsare wani mai gidan haya a bisa zargin yin lalata da wata yarinya ’yar shekara shida, ɗaya daga cikn masu zaman haya a gidansa.

An gurfanar da mutumin ne mai suna Musibau Lamidi mai shekara 50 a kan zargin lalata yarinyar da aka boye sunanta da iyayenta ke haya a gidansa a Unguwar Olode da ke Ibadan.

Yayin gabatar da karar, Lauyan ’Yan sanda Gbemisola Adedeji ya shida wa kotun cewa, wanda ake zargi ya aikata laifin ne a tsakanin ƙarfe 8 na safe zuwa 4 na yammacin ranar 13 ga watan Maris na bana, yayin da mahaifiyar yarinyar ta fita ta bar ta a gida lokacin da ta je neman ɗakin da za su koma sakamakon tashinsu da ya yi.

KU KUMA KARANTA: Yaron gida ya faɗi, ya mutu, bayan uwargidansa ta tilasta shi ya yi lalata da ita

Amma bayan tafiyarta sai wanda ake zargin ya shiga ɗakinsu inda ya yi lalata da yarinyar, wanda hakan ya saba wa Sashe na 34 na Dokar Kare Hakkin Yara ta Jihar ta Shekarar 2006, wanda ake zargi ya musanta aikata laifin.

Alkalin Kotun Misis S.A Adesina ta bayar da umarnin a tsare wanda ake zargi a gidan gyaran hali na Agodi har sai ta ji daga bakin Babban Mai gabatar da kara na Jihar kan batun ta kuma sa ranar 25 ga watan Afrilu don ci-gaba da sauraron karar.

Leave a Reply