Korar Malaman Makaranta A Kaduna: An Kalubalanci Sanata Uba Sani

0
346

KWAMITIN da ke fafutukar Yakin neman zaben dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna, Honarabul Isa Ashiru Kudan, ta kalubalanci Sanata Uba Sani na APC sakamakon kasa yin maganar da ya yi game da lamarin korar malaman makaranta a Jihar Kaduna.

A cikin wata takardar da kwamitin Isa Ashiru ta fitar da aka rabawa manema labarai, kwamitin ta kalubalanci Uba Sani bisa yin shuru, ya yi Gum da bakinsa yaki cewa komai a game da lamarin korar malaman makaranta da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi duk da cewa shi ne dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Kaduna.

Takardar mai dauke da sa hannun Daraktan fadakarwa da yayata manufofin dan takarar Gwamna Isa Ashiru, Yakubu Lere El-Saed ya Sanya wa hannu, ta bayyana cewa malaman makaranta sama da dubu biyu aka sallama a Jihar Kaduna kwanan nan.

Lere ya ci gaba da cewa ana kuma shirin yin Rusau a kasuwar Gwari da ke unguwar Rigasa da kasuwar garin Saminaka a karamar hukumar Lere.

“Saboda haka ne muke ganin yin shuru da Sanata Uba Sani ya yi wata alamace da ke nunin cewa zai ci gaba da aiwatar da ayyuka irin wannan da El-Rufa’I ya ke yi, wanda mai yuwuwa ne takensa shi ne ci gaba da aikin da Gwamna El-Rufa’I ke aiwatarwa.

“Hakika ya dace kowa ya sani cewa wannan kokari ne na ganin bayan ci gaban ilimin Firamare a Jihar Kaduna. Saboda alkalumman da ake da su game da batun harkar ilimi na tabbatar da cewa komai ya lalace idan aka yi la’akari da takardar kammala karatu domin akwai koma baya kwarai a zamanin mulkin Gwamna Nasiru El-Rufa’I, saboda mutum zai yi ta tunanin cewa shin wai me ta ke son cimma wa da irin wannan aikin na korar Malaman makaranta?

“Muna tausayawa wadanda wannan lamarin korar malaman makaranta ya shafa wato jama’ar Jihar Kaduna, malaman makarantu da kuma kungiyar NUT sakamakon kashe harkar ilimi baki daya a Jihar, kuma da wannan ne muke kokarin tabbatar maku da cewa idan Honarabul Isa Ashiru Ashiru ya samu nasarar zama Gwamnan Jihar Kaduna, za a yi maganin irin wannan kuma a inganta lamarin ilimin a Jiha baki daya.

“Muna kira tare da ba su hakurin cewa su bar komai ga Allah kuma muna kira a gare su da su tabbatar kowa ya yi rajista domin ganin bayan irin wadannan abubuwan na Gwamnatin APC a Jihar”, Cewar Daraktan wamitin Yakin neman zaben Isa Ashiru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here