Aminu Goro Da Injiniya Abubakar Kabir Bichi Za Su Samar Da Nasarar APC A 2023

0
408

ALAMU suna Kara nunar da cewa Jam’iyyar APC mai mulkin kasarnan ta na kara yin karfin lashe zabukan da ake shirin gudanarwa a shekara ta 2023 idan Ubangiji ya kaimu, musamman yadda wasu daga cikin mutanen da Jam’iyyar ta tsayar takara kan mukamai daban-daban suke ci gaba da bunkasa Jam’iyyar.

A matsayina na daya daga cikin yan kasa kuma mai ikon yin sharhi kan al’amuran dake faruwa, yana dakyau in yabawa magoya bayan jam’iyyar ta APC musamman shugabanni da masu ruwa da tsaki saboda jajircewa da aka yi wajen fitar da yan takara masu nagarta wadanda kuma suke da goyon bayan al’umma.

Wannan ce ta sanya naga ya dace in dan bayyana sahihancin wasu daga cikin yan takarar da aka tsayar duba da yadda suke kokari da gaske wajen gudanar da wakilcin mazabun su tun lokacin da suka fara wakilcin al’umominsu a majalisun kasa.

Haka kuma bisa dukkanin alamu, tsarin da Jam’iyyar APC ta yi zai taimaka wajen bata nasara sosai a zaben 2023 wanda zai kasance cikin yanayi mai kyau da gamsarwa ta kowane bangare na wannan kasa duk da cewa jam’iyyu da dama sun tsayar da yan takarar su.

A jihar mu ta Kano, na yaba sosai bisa yadda gwamna Abdullahi Umar Ganduje da dukkanin masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar su ka yi namijin kokari wajen samar da yan takara masu kyau da nagarta domin shiga zabe domin samarda wakilci mai inganci.

Akwai yan takarar da aka tsayar guda biyu wadanda ko shakka babu nake yi masu kallon riba ga al’umomin su, idan har aka zabe su kan mukamai daban-daban domin ganin dimokuradiyya tana samar da riba mai amfani ga al’umma kamar yadda aka ga kamun ludayin su.

A karamar hukumar Bichi, an tsayar da Injiniya Abubakar Kabir Abubakar wanda aka fi sani da (Abban Matasa) wanda daga shekara ta 2019 zuwa yau ya samar da managarcin ci gaba a mazabu ba tare da nuna bambancin ra’ayi ko bangare ba.

Muna matukar alfahari da wannan wakili wanda kuma zuwansa ya samar da alheri mai yawa a sassa daban-daban na fadin karamar hukumar Bichi, don haka muna fata cewa al’ummar wannan yanki namu zasu sake zabar Injiniya Abubakar Kabir Abubakar da Jam’iyyar APC domin dorawa kan abubuwan da ya faro.

Haka kuma ina mai amfani da wannan dama wajen bayyana cewa tsayar da Kwamared Aminu Suleiman Goro a matsayin dan takarar majalisar wakilai ta tarayya daga karamar hukumar Fagge, wanda tun a shekara ta 2011 yake wakiltar wannan yanki kuma ya yi abubuwa masu yawan gaske domin kyautata rayuwar al’ummar sa.

A karshe, ina kara jinjinawa mai girma Gwamna, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da dukkanin shugabannin Jam’iyyar APC saboda yadda aka hada hannu ake tafiyar da jam’iyyar cikin yanayi mai kyau da gamsarwa, sannan zamu ci gaba da bada goyon bayan mu wajen tabbatar da cewa an gudanar da zabukan shekarar 2023 mai zuwa, lami lafiya.

Alhaji Usman B.Dangwari,
Rijiyar Lemo Quarters, Kano.

Email: medialink57@yahoo.com

Leave a Reply