Ko kasan maganin ciwon haƙori sadidan?

A Samu itacen tumfafiya a  dafa da jar kanwa a kurkura  da ɗuminsa safe da yamma har kwana uku, haƙora za su warke.

Kogon haƙori

A nemi audugar cikin ƙwallon tumfafiya a dangwali nonon ta kaɗan a sa cikin kogon, a riƙa yin haka lokaci bayan lokaci, kogon zai cike, (Amma fa akwai zafi)

Tsutsar haƙori

A tafasa saiwar tumfafiya a kurkura baki da ɗumunsa, sau uku a rana kwana biyu, za’a rabu da ita.

Haƙora mai jini

A dafa sassaƙen tumfafiya da ganyenta a sa gishiri kaɗan, a kurkura baki da ɗumi-ɗumi sau uku a rana kwan ɗaya za’a yi, haƙora za su daina jini.

KU KUMA KARANTA: Maganin dafin cizon Maciji da na guba

Warin baki

A dafa ruren Tumfafiya da ƙwallonta idan ruwan ya huce a sa abin wanke baki (Brush) ana wanke bakin bayan an ɗan sa ruwan. Insha Allah kayi ban kwana da warin baki.

Hasken haƙori

A shanya furen Tumfafiya idan ya bushe a maida shi gari a haɗa shi da alaf kaɗan, a dangwala da buroshi ko asuwaki a wanke baki. Haƙora za su yi fari tas.

Dattin goro ko hayaƙin taba

A dafa furen tumfafiya da lemun tsami (Lime) a wanke baki da shi da a bin wanke baki (Brush). Dattin zai fita daga baki gaba ɗaya.


Comments

4 responses to “Ko kasan maganin ciwon haƙori sadidan?”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Ko kasan maganin ciwon haƙori sadidan? […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Ko kasan maganin ciwon haƙori sadidan? […]

  3. […] KU KUMA KARANTA: Ko kasan maganin ciwon haƙori sadidan? […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *