Ko kasan Farfesa mai sana’ar wanzanci da ba da maganin gargajiya a Najeriya?

‘Farfesa Bashir Aliyu Sallau, fitaccen Malami ne wanda ya kai matsayin Farfesa a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsin-Ma ta jihar Katsina. A wata tattaunawa da ya yi da gidan Rediyon DW Hausa, ya bayyana yadda yake haɗa sana’arsa ta wanzanci da kuma koyarwa a jami’a.

Farfesa Sallau, wanda yake tsangayar nazarin Harsuna (Languages) a jami’ar, shi Farfesa ne a ɓangaren yaren Hausa. Ya bayyana cewa, yana yin sana’arsa ta wanzanci ne bayan ya gama koyarwa a jami’a na lokutan da aka ware masa na koyarwa.

KU KUMA KARANTA: An kama marar lafiyan da ya sace motar ɗaukar gawa a Asibiti

Farfesan ya ce “kasan koyarwa a jami’a ba irin sauran aikin gwamnati bane, wanda za’a ce ka tafi ƙarfe 8:00 na safe, ka dawo ƙarfe ka dawo ƙarfe 4:00 na yamma. Ita Jami’a kowane Malami ana ba shi lokuta ne da zai yi koyarwa.To a lokutan da nake da su, waɗanda ba na shiga aji ba, sai na tafi sana’a ta, ta wanzanci.

Wani lokacin da safe, wani lokacin kuma da yamma. Zan ci gaba da sana’a ta, ta wanzanci, saboda muhimmancinta a rayuwata”.Ya ci gaba da cewa “tun kafin Bature ya zo ƙasar Hausa, ƙasar Hausa tana da sana’o’i waɗanda suke taimaka mata wajen haɓakar tattalin arziƙinta. Sana’ar wanzanci wanda Allah ya ɗora ni akan ta, ina alfahari da ita. Sana’ar wanzanci, duk wanda ya sanni, ya sanni da ita. Bayan wanzanci, ina cire haƙƙin wuya da beli a mata, sannan ina yin ƙaho da sauran ayyukan wanzanci.

Kuma ina ba da magungunan gargajiya, har yanzu ban daina ba.Duk inda aka neme ni wajen sana’ar wanzanci, ina zuwa. Na fahimci a cikin sana’ar wanzanci akwai arziƙi.

A lokacin da Malaman jami’o’i ƙasar nan suka tafi yajin aiki, sai da aka yi wata Takwas ba a ba mu albashi ba, to sana’ar wanzanci ce ta riƙe ni a tsawon waɗancan watannin, ko kaɗan ban takura ba. Sai na ɗauki Zabira ta, na tafi sana’a ta, ta wanzanci.Wannan shi ne ya ƙara min ƙarfin gwiwa, na ƙara riƙo da wannan sana’a wadda na gada. Domin duk wanda ya yasar da sana’ar da ya gada, yana cikin tashin hankali.

Ni ma duk ‘ya’yana suna wannan sana’a ta wanzanci, kuma duk sun yi karatun Bokon” inji shi.Farfesa Bashir ana ta mamakinsa, ganin yadda ya rungumi sana’ar da ya gada ta wanzanci, duk da matsayinsa na wanda yake da ƙololuwar matsayi a duniyar wato Farfesa, saɓanin sauran takwarorinsa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *