Bayan yanke musu hukunci kan tuhumar su biyun da akeyi da lefin kisan Sheikh Bagoni, rundunar sojojin Najeriya ta kori sojojin biyu da aka tura bataliya ta 241 Recce, Nguru, jihar Yobe.
Laftanal Kanal Ibrahim Abdullahi Osabo, muƙaddashin kwamandan bataliyar ya bayyana cewa an samu waɗanda ake tuhumar da laifuka biyu: rashin ɗabbaka aikin soja yadda ya kamata, da kuma yin abin da ya kawo ƙaskanci ga tsarin aikin tsaro.