Idan Matasan Najeriya Suka Rungumi Fanni Kafofin Sadarwar Zamani Za Su Sami Ayyukan Yi – Habibu Mu’azu

0
374

Daga; Isah Ahmed, Jos.

HABIBU Mu’azu shi ne Daraktan cibiyar yada labarai ta kafofin sadarwar zamani na Enactifix da ke garin Jos. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana cewa idan matasan Najeriya suka rungumi fanni kafofin sadarwa na zamani, zasu sami ayyukan yi.

Ga yadda tattaunawar ta kasance

GTK: Mene ne makasudin kafa wannan cibiya?

Habibu Mu’azu: Makasudin kafa wannan Cibiya, shi ne ganin yadda aka tafi aka bar Arewa a baya a bangaren harkokin sadarwar zamani ya sanya muka yi tunanin kafa wannan cibiya, musamman a wannan gari na Jos domin mu rika yada labarai na gaskiya, ba tare da nuna bangaranci ko banbancin addini ba. Kuma mun dauki lokaci muna shirin kafa wannan cibiya, domin mun fara shirin kafa wannan cibiya, tun shekara ta 2009. a lokacin na fahimci cewa lallai akwai bukatar al’ummarmu ta sami irin wannan cibiya.

GTK: Wadanne abubuwa ne wannan cibiya ta kunsa?

Habibu Mu’azu: A wannan cibiya muna daukar labarai tare da yada su. Kuma muna shirin rediyo da Talabijin, kuma dukkan abubuwan da muke yi, muna sanya su ne a kafofin sadarwar zamani na sada zumunta na yanar gizo.

GTK: Daga lokacin da kuka kafa wannan cibiya zuwa yanzu, ya kuka ga yadda mutane suke bibiyarku?

Habibu Mu’azu: Gaskiya mafiya yawan masu bibiyarmu matasa ne domin kusan dukkan shirye-shiryen da muke yi, sun shafi matasa ne. Don haka matasa ne suka fi bibiyarmu, kuma wadannan matasa sun hada da nan Najeriya da kuma kasashen waje domin muna da matasa da suke bibiyarmu a kasashen Libya da Amerika da Jamus da Saudiya da Sudan da Lebanon da dai sauransu.
Kuma muna watsa shirye – shiryenmu da harsunan Turanci da Hausa.

GTK: Kuna da ma’aikata guda nawa a wannan cibiya?

Habibu Mu’azu: Ya zuwa yanzu muna da ma’aikata kusan mutum 13, wadanda kullum suke fita su samo mana labarai.

GTK: Mene babban burinku kan wannan cibiya?

Habibu Mu’azu: Babban burinmu shi ne muga cewa al’ummarmu ta gyaru, ta dauki hanya ta cigaba.

GTK: A matsayinka na masani kan kafofin sada zumunta na zamani, ya kake ganin yadda wannan bangare zai kasance nan gaba?

Habibu Mu’azu: Wato kafofin yada labarai da muka saba da su a baya, kamar Rediyo da Talbijin da Jaridu, yanzu zamani yazo da wani canji kan wadannan kafofin yada labarai. Yanzu komai na labarai ya koma kan wadannan kafofin yada labarai na zamani na yanar gizo.

Yanzu labarai na komai ya koma wayar hanu kuma kullum abin gaba yake yi, don haka ina ganin nan gaba, wadannan kafofin yada labarai da muka sani a baya wato Rediyo da Talbijin da Jaridu za a neme su a rasa.

GTK: A matsayinka na masani kan kafofin sadarwa na zamani, wace gudunmawa ce kake ganin wannan fanni zai bayar wajen samar da ayyukan yi ga matasan kasar nan?

Habibu Mu’azu: Wato wannan fanni na kafofin sadarwa na zamani, a yanzu yana kan gaba wajen samarwa matasa ayyukan yi. Akwai sana’o’i da dama da mutum zai yi da waya wadanda nan take zasu kawo masa kudade.

A duniyar yanzu, akwai mutane da dama da suke sana’o’i na gaskiya bana damfara ba, ta wannan fanni. Babu shakka idan matasan Najeriya suka rungumi wannan fanni, na hanyoyin sadarwar zamani, zasu sami ayyukan yi. Matasa kada su damu da cewa sai sun yi aikin Gwamnati, domin yanzu duk matashin da ya ce yana jiran aikin Gwamnati, yana yaudarar kansa ne.

Matasa su shiga kafofin sadarwar zamani zasu sami ayyukan yi domin yanzu idan ka dubi masu kudin duniya, zaka ga cewa masu harkokin kasuwanci ne a kafofin sadarwar zamani. Misali kamar Elon Reeve Musk da Jeff Bezos mai kamfanin Amazon da Mark Eliot Zuckerberg mai shafi Facebook, duk sun sami kudadensu ne ta hanyar kafofin sadarwar zamani.

GTK: Wanne kira ne kake da shi zuwa ga Gwamnati da al’ummar Najeriya, kan wannan fanni na kafofin sadarwar zamani?

Habibu Mu’azu: Ina kira ga Gwamnatoci kan su samar da cibiyoyin horar da ilmin kafofin sadarwar zamani, saboda mahimmancin da wannan fanni yake da shi. Kuma ina kira ga Gwamnatoci su sanya a rika koyar da wannan fanni a makarantunmu, domin matasa su koyi wannan fanni kamar yadda ya kamata

Kuma ina kira ga al’ummar Najeriya musamman na Arewa, mu farka daga barcin da muke yi kan wannan fanni na kafofin sadarwar zamani.

Leave a Reply