Hushpuppi zai kwashe shekaru 11 a gidan yari

An ɗaure Fitaccen ɗan Instagram, Ramon Abbas da aka fi sani da HUSHPUPPI, shekaru 11 a gidan yari a Amurka.

A cikin ƙarar ƙarshe da alkali Otis Wright ya yanke masa hukunci a ranar 19 ga Satumba, Hushpuppi ya rubuta wa kotu wasiƙa ta sirri yana ba da labarin tushen arzikinsa, laifukan da ya aikata, da kuma nadama da yayi.

Ya kuma nemi afuwar ‘yan uwansa da ya ja musu abin kunya, yayin da ya yabawa hukumar binciken manyan laifuka ta ƙasa (FBI) da ta yi ƙwakkwaran aiki na gurfanar da shi a gaban kuliya.

A ranar 19 ga Satumba, Alkali Otis Wright ya jinkirta yanke hukuncin Hushpuppi zuwa ranar 3 ga Nuwamba.

Da farko dai Alƙalin ya ƙi amincewa da buƙatar da wanda ake ƙara ya nema na a jinkirta yanke hukunci inda a ƙarshe dai kotun lardi ta Amurka da ke California ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 11 a gidan yari.

Amma Hushpuppi zai shafe shekaru tara a gidan yari saboda ya shafe shekaru biyu a Amurka bayan kama shi a Dubai a shekarar 2020.

Gwamnatin Amurka a watan da ya gabata ta buƙaci kotun lardi da ke tsakiyar California ta yanke wa Hushpuppi hukuncin ɗaurin watanni 135 a gidan yari saboda zamba.

Gwamnatin ta bayyana dalilanta na gabatar da kwatankwacin ɗaurin shekaru 11 da watanni uku ga Raymon Abbas a cikin ƙarar da ta shigar a gaban kotun.

Hushpuppi ya kasance ɗaya daga cikin masu tsaftar muhalli a gidan yarin da ake tsare da shi tun bayan kama shi a shekarar 2021.


Comments

One response to “Hushpuppi zai kwashe shekaru 11 a gidan yari”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *