Hukumar tace fina-finai a Kano ta kama matashi da budurwar da suke baɗala a soshiyal midiya
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano karkashin jagorancin shugabanta Alh. Abba El-mustapha ta samu nasarar kama wani matashi tare da wata budurwa da suka dade suna yada fitsara a kafafen sada zumunta na zamani a Jahar Kano.
A cewar Shugaban Hukumar Abba El-mustapha tsawon lokaci Hukumar ta dauka domin kama wannan matasa da ake zargi wato Mai suna Ahmad ‘Anayi da Maryam ‘Madogara’ kan yin bidiyon da basu dace ba kasancewar sunci karo da tarbiyar malam Bahaushe tare da koyarwar addinin musulunci.
KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Filato ta dakatar da haƙar ma’adinai saboda matsalar tsaro
Sanarwar da kakakin hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya sanyawa hannu tace Alh. Abba El-mustapha ya ce Hukumar bazata saurarawa wannan matasa ba, domin ta gama tattara bayanai dan aikawa dasu gaban kotu domin girbar abinda suka shuka.
Abba El-mustapha ya kara da cewa ko kusa ko alama Hukumar bazata lamunci yin fitsara a kafafen sada zumunta na zamani ba, inda yace Hukumar ta kirkiri wani sashi na musamman a cikin wannan shekarar ta 2025 domin yin fito na fito da duk wanda suke zubarwa da Jahar Kano mutunci a kafafen sada zumunta na zamani.
El-mustapha ya kuma yi al’kawarin cewa Hukumar zata cigaba da yin aikinta babu sani babu sabo, ya kuma bukuci mazauna Kano dasu cigaba da bawa Hukumar hadin kai kamar koda yaushe.