Hukumar kwastam sun kama mazakutar jakuna 7000 da za a fitar birnin Hong Kong

1
475

Hukumar kwastam a Najeriya, ta ce ta yi nasarar hana fita da mazaƙutar jakuna 7000 da aka yi shirin safarar su zuwa Hong Kong. Kwastam ta yi wawan kamun ne ranar Laraba a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke birnin Lagos.

Buhunan da aka ɓoye hajar

Kwantirola mai kula da filin jirgin sama, Sambo Dan Galadima ne ya tabbatar da hakan a tattaunawarsa da BBC ranar Laraba, yana mai cewa an naɗe mazakutar jakunan ne a cikin buhunhuna 16. Dan Galadima ya ƙara da cewa waɗanda ake zargi da yunƙurin safarar kayan sun tsere daga filin jirgin, a lokacin da jami’an kwastam suka nuna shakkun kan abin da ke cikin buhunhunan, sakamakon warin da ya turnuƙe wurin lokacin binciken kayan. Darajar kayan dai ta kai sama da naira, 216,212,813.58.

Najeriya ta haramta safarar fatu ko duk wani abu da ya shafi jaki zuwa ƙasashen ƙetare, sakamakon ƙarancin su da ake fuskanta a ƙasa. Ƙasashen yankin Asiya kamar China, yankin Hong Kong, da Koriya ta Kudu, da sauransu, na amfani da shi wajen yin magungunan gargajiya.

1 COMMENT

Leave a Reply