Hukumar Hisbah ta kama mata da maza 23 a wuraren da basu daceba a Nasarawa GRA

1
246

Daga Shafaatu DAUDA, Kano

Dakarun hukumar Hisbah na jihar Kano masu hani ga munanan aiyuka, da kuma yin nuni ga kyakkyawa, a daren jiya ne su ka kai sumame a gidaje 3 da ake zargin samari da yan mata kan hadu su sha shisha da sauran kayan maye, daga bisani su aikata masha’a.

Tun da fari, Babban kwamandan hukumar Hisbah, Dr Harun Muhammad Sani Ibn sina yace maƙwabtan waɗanan gidaje da ake zargi sune suka kaiwa hukumar ƙorafi, a lokuta daban-daban, tare da nuna takaicin yadda ake barin ƙananan yara shiga irin wancan gida.

A lokacin sumamen an sami nasarar cafke matasa 23 maza 4 sai yan mata 19 a lokacin da suke tsaka da busa tabar shisha, inda Dakarun Hisbah ba su yi wata-wata ba su ka damƙo su izuwa shalkwatan hukumar Hisbah.

Binciken da dakarun Hisbah na farin kaya su ka gabatar, ya tabbatar da cewa ana Shan shisha da sauran kayan sa maye, baya ga aikata badaƙala a gidan.

Wuraren da aka damƙo matasan sun hadar da na titin Tukur road a unguwar nasarawa, da na titin sultan road, shi ma a unguwar nasarawa, da Kuma zuwa asibitin Nasarawa wato hospital road.

A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran hukumar Lawan Ibrahim fagge ya aikowa Neptune prime, yace Babban kwamandan hukumar Hisbah, Dr. Muhammad Sani Ibn Sina ya yi tsokaci, inda ya ba da tababbacin cigaba da kai sumame har ma da ɗaukan matakan shari’a a kan irin waɗannan gidajen.

Sannan ya gargadi iyaye tare da Jan kunnen matasa da su guji jefa kan su cikin aiyukan masha’a domin samun shuwagabanni na gari.

1 COMMENT

Leave a Reply