Hukumar EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Delta kan badaƙalar tiriliyan ₦1.3

0
13
Hukumar EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Delta kan badaƙalar tiriliyan ₦1.3

Hukumar EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Delta kan badaƙalar tiriliyan ₦1.3

Hukumar EFCC za ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, kan zargin ruf-da-ciki kan Naira tiriliyan ɗaya da biliyan 300.

EFCC na zargin Okowa da karkatar da kuɗaɗen ne daga kason 13% na kuɗaɗen ɗanyen mai da da warware don bunƙasa yankuna masu arzikin mai ma Nijeriya, a lokacin da yake Gwamnan Delta.

Okowa shi ne ɗan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na babbar adwa ta Jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2023 a Nijeriya.

A ranar Litinin ne EFCC ta tsare, ta ci gaba da yi masa tambayoyi a ofishinta da ke Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

KU KUMA KARANTA: EFCC Ta Cafke Akanta Janar Na Kasa, Ahmed Idris Bisa Zargin Badakala Naira Biliyan 80

Kakakin EFCC, Dele Oyewale ya tabbatar cewa, “Tabbas Sanata  Ifeanyi Okowa yana hannunmu, muna tsare da shi.”

Majiyoyi a Hukumar sun bayyana cewa tsohon ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasan na Jamiyyar PDP, ya jima yana zuwa ofishin EFCC amsa tambayoyi, kafin a ƙarshe ta tsare a ranar Litinin.

Ana sa ran ranar Talata hukumar za ta gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin karkatar da kuɗaɗen.

Wasu ’yan cikin gida a hukumar sun bayyana cewa an faɗaɗa binciken zuwa kan wasu manyan jami’an Ma’aikatar Kudi da na Hukumar Bunƙasa Yankuna Masu Arzikin Ɗanyen Mai (DESOPADEC) da suka ya aiki a zamanin mulkin Okowa a Jihar Delta.

Wasu jami’an EFCC sun ce a halin yanzu hukumar tana bincikar ’yar Okowa, Marilyn Okowa-Daramola, mai wakiltar yankin Delta ta Arewa maso Gabas a majalisar dokokin Jihar, a sakamakon takardar ƙorafe-ƙorafe da aka shigarta kan mahaifinta.

Ana zargin tsare tsohon Gwamna Ifeanyi Okowa ya kaɗa hantar ’yan siyasa da dama a Jihar Delta, inda ake ci gaba da jiran ganin yadda za ta kaya.

Leave a Reply