Hukumar EFCC ta cafke ma’aikatan banki 12 da zargin satar kuɗi

1
762

Hukumar yaƙi da almundahana a Najeriya ta EFCC ta kama ma’aikatan banki 12 da zargin satar kuɗaɗe a wuraren aikinsu a Jihar Enugu da ke kudancin ƙasar.

A cewar hukumar, binciken farko-farko da ta gudanar ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun saci kuɗaɗe daga wasu asusu da ba sa aiki a wani daga cikin reshen bankunan da a yanzu ba sa aiki a jihar ta Enugu.”

An tura kuɗaɗen daga asusan da ke rufe zuwa ga mutane daban-daban, kuma tuni EFCC ta gano wanda ya fi kowa samun rabo mai tsoka,” a cewar sanarwar da hukumar ta fitar ranar Asabar.

Mutanen waɗanda suka ƙunshi mata huɗu da maza takwas, an kama su ne a ranar Juma’a kuma za su gurfana a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

An bayyana sunayensu da: Odeniyi Anthony, Deki Kingsley Onyekachi, Oguchukwu Ene, Elendu Chizaram, Anyakora Uchenna, Onah Kingsley, Akwe Elizabeth and Chinenye Grace Acibe, Victoria Ezedie, Chidi-Ukah Obinna, Etoh Lawrence Uzochukwu, Udeze Harrison.

1 COMMENT

Leave a Reply