Hukumar ‘yansanda sun ceto mutane 77 daga coci a Jihar Ondo

1
598

Rundunar ‘yan sandan Jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ce ta ceto mutum aƙalla 77 akasrinsu yara ƙanana daga wata coci a jihar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Ondo, SP Funmilayo Odunlami, ta bayyana cewa an tara mutanen ne a cocin, tsawon watanni bisa alƙawarin cewa Yesu Almasihu zai sake bayyana yayin wata lacca da za a gudanar.

Ta ƙara da cewa sun kama babban faston cocin da ke yankin Valentino da mataimakinsa.

Tun farko rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Asabar cewa tana bincike kan rahoton “sace yara masu yawa” a yankin na Valentino.

Rundunar ‘yan sandan ta ce wasu daga cikin mutanen da aka ceto sun kasance a cocin tun daga watan Janairun 2022, inda suke kwana a gidan ƙarƙashin ƙasa.

“An faɗa musu cewa za a gudanar da lacca a watan Afrilu inda a wurin ne Yesu Almasihu zai dawo, ” a cewar SP Odunlami. “Amma kuma daga baya aka ce musu sai Disamba za a yi laccar.

“Mahaifiyar wani yaro daga ciki ta ce ɗanta ya ɓata tun a watan Janairu kuma an gan shi a wurin.”

Haka nan, wasu iyaye sun faɗa wa ‘yan sanda cewa ‘ya’yansu sun daina zuwa makaranta saboda jiran dawowar Yesu da cocin ta alƙawarta musu.

1 COMMENT

Leave a Reply