Hukumar ‘yansanda sun ceto mutane 77 daga coci a Jihar Ondo

Rundunar ‘yan sandan Jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ce ta ceto mutum aƙalla 77 akasrinsu yara ƙanana daga wata coci a jihar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Ondo, SP Funmilayo Odunlami, ta bayyana cewa an tara mutanen ne a cocin, tsawon watanni bisa alƙawarin cewa Yesu Almasihu zai sake bayyana yayin wata lacca da za a gudanar.

Ta ƙara da cewa sun kama babban faston cocin da ke yankin Valentino da mataimakinsa.

Tun farko rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Asabar cewa tana bincike kan rahoton “sace yara masu yawa” a yankin na Valentino.

Rundunar ‘yan sandan ta ce wasu daga cikin mutanen da aka ceto sun kasance a cocin tun daga watan Janairun 2022, inda suke kwana a gidan ƙarƙashin ƙasa.

“An faɗa musu cewa za a gudanar da lacca a watan Afrilu inda a wurin ne Yesu Almasihu zai dawo, ” a cewar SP Odunlami. “Amma kuma daga baya aka ce musu sai Disamba za a yi laccar.

“Mahaifiyar wani yaro daga ciki ta ce ɗanta ya ɓata tun a watan Janairu kuma an gan shi a wurin.”

Haka nan, wasu iyaye sun faɗa wa ‘yan sanda cewa ‘ya’yansu sun daina zuwa makaranta saboda jiran dawowar Yesu da cocin ta alƙawarta musu.


Comments

One response to “Hukumar ‘yansanda sun ceto mutane 77 daga coci a Jihar Ondo”

  1. […] KU KUMA KARANTA:Hukumar ‘yansanda sun ceto mutane 77 daga coci a Jihar Ondo […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *