Har yanzu a ɗaure nake a sarƙa, jini baya gudana yadda ya kamata a jikina, dukda an biya kuɗin fansa miliyan 2- DPO Musa Muhd Gyaɗi-Gyaɗi

Jami’in ‘yan sanda na Dibision (DPO) da aka yi garkuwa da shi a Birnin Gwari, Kaduna, sama da kwanaki 90 da suka gabata, ya ce duk damina ta yi ta zuba a kansa.

Jami’in ya ce ba shi da lafiya, gudan jini na ya daskare, yayin da ‘yan fashin suke tsare da shi tun bayan sace shi a watan Yuni. Ɗaya daga cikin ‘yan uwa Musa Muhammad Gyadi-Gyadi ne ya bayyana hakan ga manema labarai inda ya ce suna yawan jin yadda ‘yan bindigar ke azabtar da DOP ɗin a duk lokacin da suka kira waya.

An yi garkuwa da CSP Mohammed Gyadi-Gyadi ne a lokacin da yake tuƙa mota zuwa ofishin ‘yan sanda da ke garin Birnin Gwari, hedikwatar ƙaramar hukumar Birnin Gwari.

Ya ce: “Muna magana da shi ta wayar ‘yan fashin. Jami’in ya shaida min cewa duk ruwan sama na bana yana sauka a kansa, kuma ba shi da lafiya, saboda jini baya gudana yadda ya kamata a jikinsa, saboda a ɗaure yake. “Ya roƙe mu mu ceci ransa.

Ya dai roke mu ne mu cece su, domin a halin yanzu yana yin bahaya da jini, kuma ƙafarsa na masa azabar ciwo.

“An bai wa wani mutum Naira miliyan 2 ya kai wa masu garkuwar, amma sai suka karɓi kudin suka ƙi sakin wanda yakai kuɗin”.

A cewarsa, ‘yan fashin na ci gaba da neman ƙarin kuɗi, da katin waya, da kuma babur.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *