An yi wa wani mutum duka har lahira, bayan da ya yi wa akuya fyade

0
363

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Wani matashi ɗan garin Mtunzini da ke garin KwaZulu-Natal ya gamu da ajalinsa bayan an kama shi yana lalata da wata akuya a ƙasar Afrika ta Kudu.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 00:00 na ranar Litinin, 5 ga Satumba, 2022.

A cewar 1KZNTV  News, mutumin ya so yi wa wata mata ‘yar shekara 61 fyade a lokacin da ya yi yunkurin kutsawa cikin gidanta amma ta yi nasarar fafatawa tare da yin barazanar yanke kan mutumin.

Biyo bayan yunƙurin kutsawa cikin gida da aka yi, matar ta ji karar kukan akuyar, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Bayan bincike da aka yi, an kama mutumin da hannu wajen yi wa akuyar fyade.

Daga nan ne ‘yan unguwar suka taru a gidan toshewar inda suka ɗauki doka a hannunsu ta hanyar lakaɗawa mutumin duka har lahira.

Leave a Reply